DUNIYA
3 minti karatu
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Shugaban Rasha ya shaida wa takwaransa na Amurka cewa bai wa Kieve makamai masu linzami samfurin Tomahawk ba zai sauya komai a fagen yaƙin ba amma zai iya lalata dangantakar diflomasiyya da hana zaman lafiya.
Putin ya gargaɗi Trump cewa bai wa Ukraine makamai mai linzamin Tomahawk zai jawo matsala tsakaninsu
Putin ya shaida wa Trump cewa duk wani mataki na Amurka na bai wa Ukraine makamai masu linzami na Tomahawk zai raunata dangataka tsakanin ƙasashen / AP
19 awanni baya

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya shaida wa takwaransa na Amurka cewa duk wani mataki na bai wa Ukraine makamai masu linzami masu dogon zango na Tomahawk zai illata dangantaka tsakanin Moscow da Washington.

"Putin ya ƙara nanata tunaninsa cewa makamai masu linzamin Tomahawk ba za su sauya yanayin da ake ciki a filin yaƙi ba, amma zai iya ta’adi mai yawa ga dangantaka tsakanin ƙasashenmu biyu, ballanta yiwuwar sansatawa cikin zaman lafiya a Ukraine," kamar yadda mai taikama wa shugaban Rasha Yuri Ushakov ya shaida wa manema labarai a lokacin wani jawabi a Moscow ranar Alhamis.

Ya ce tattaunawa ta waya da shugabannin suka shafe kusan sa’o’i biyu da rabi suna yi ta kasance ta "gaskiya ce, kuma ta ƙeƙe da ƙeƙe da kuma ta yarda."

Ushakov ya ƙara da cewa sun mayar da hankali kan yaƙin da ake a Ukraine, inda Putin ya bai wa Trump abin da ya kira "ciakakken bayanin yadda lamarin yake a halin yanzu."

Mai taimaka wa shugaban ya ce Moscow ta shaida wa Washington cewa dakarun Rasha suna riƙe da "cikakken muhimmin iko" a fagen daga, yayin da Trump ya yi ta jaddada buƙatar samun zaman lafiya cikin gaggawa a rikicin.

"Ɗaya daga cikin muhimman bayanan shugaban na Amurka shi ne kawo ƙarshen yaƙi a Ukraine zai buɗe babban — ya jadada shi — yiwuwar gina dangantaka ta tattalin arziƙi tsakanin Amurka da Rashsa," in ji Ushakov.

Ya ƙara da cewa shuwagabannin biyu sun tattauna yiwuwar sake wata tattaunawa ta ido da ido kuma sun amince cewa jami’ai daga ɓangarorin biyu za su fara shiri domin wani taro, inda aka ambaci Budapest, bababn birnin Hungary, a matsayin inda za a yi shi.

Haɗuwar Putin da Trump ta baya-bayan nan dai an yi ta ne a watan Agusta a wani taro a Alaska, amma ƙoƙarin ci gaba da tattaunawar zaman lafiya ta ci tura.

Tuni dai Trump ya nemi ya haɗa kai da ƙawayen NATO domin ƙara matsin lamba kan Moscow, ciki har da neman kawo ƙarshen sayan man Rasha.

Bayan tattaunawar waya ta ranar Alhamis, Trump ya wallafa wani saƙo a shafinsa na sada zumunta na Truth Social inda ya ce shi da Putin suna shirina haɗuwa a Hungary domin "tattauna kawo ƙarshen yaƙin" bayan tawagar wakilai daga ɓngarorin biyu sun hallara mako mai zuwa.

Tattaunawar ta zo ne gabannin ganawar Trump da Shugaban ƙasar Ukraine Volodymyr Zelenskyy, da za a yi ranar Juma’a a fadar White House, inda za a mayar da hankali kan tattauna batun tsarin tsaro na sama da kuma makamai masu dogon zango.

Daga  farkon wannan watan, Trump ya ce ya kusa yanke shawara kan ko zai ba da izinin ba da makamai masu linzami na Tomahawk ga Kiev, wani abin da Zelenskyy ya fara nema a watan Satumba .