Sau 27 Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna suka kutsa cikin harabar Masallacin Kudus da ke Gabashin Kudus da aka mamaye a watan da ya gabata, kamar yadda bayanan hukuma da aka fitar ranar Laraba suka nuna.
Ma’aikatar Kula da Waqafi da Harkokin Addini ta Falasɗinu ta bayyana a cikin rahotonta na wata-wata cewa sojojin Isra’ila da Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna sun kutsa kai cikin wannan wuri da ake yawan takaddama a kansa, inda suka gudanar da ibadun Talmudic da raye-raye da kuma bayar da hadaya na tsirrai a cikin harabar masallacin a watan Oktoba.
Tun bayan da ya hau kujerar Ministan Tsaron Cikin Gida na Isra’ila a shekarar 2022, shugaban bangaren masu tsattsauran ra’ayi, Itamar Ben-Gvir, ya kutsa kai cikin harabar Masallacin Kudus sau 13, ciki har da sau 10 tun bayan fara yakin Isra’ila da Gaza a watan Oktoban 2023, kamar yadda ma’aikatar ta bayyana.
Masallacin Kudus shi ne wurin ibada na uku mafi tsarki ga Musulmi a duniya. Yahudawa suna kiran wannan wuri da suna Temple Mount, suna ikirarin cewa wurin ya kasance wajen haikalin Yahudawa guda biyu a zamanin da.
Isra’ila ta mamaye Gabashin Kudus, inda Masallacin Kudus yake, a lokacin yakin Larabawa da Isra’ila na shekarar 1967. Ta hade dukan birnin a shekarar 1980, amma wannan matakin bai taba samun amincewar al’ummar duniya ba.
Sojojin Isra’ila sun kara yawan ziyarce-ziyarce masu tayar da hankali
Ma’aikatar Falasɗinu ta kuma bayyana cewa sojojin Isra’ila sun hana yin kiran sallah a Masallacin Ibrahimi da ke tsohon birnin Hebron a yankin Yammacin Kogin Jordan da aka mamaye sau 96 a watan da ya gabata.
A cewar rahoton, Masallacin Ibrahimi ya sha ganin yadda aka daga tutocin Isra’ila da ziyarce-ziyarce masu tayar da hankali daga sojojin Isra’ila, da kuma sanya kayan ibada kamar su teburin Torah, masu yanka itace, kujerun roba, tanti, makirufo, da kayan kida.
Hare-haren Isra’ila sun kara tsananta a fadin yankin Yammacin Kogin Jordan tun watan Oktoban 2023, inda aka kashe Falasɗinawa fiye da 1,065 tare da jikkata kusan 10,000, kamar yadda alkaluman Falasɗinu suka nuna.
A cikin wani hukunci mai muhimmanci a watan Yuli da ya gabata, Kotun Duniya ta Bayar da Shari’a ta bayyana mamayar Isra’ila a yankunan Falasɗinu a matsayin haramun, tare da kiran a kwashe dukkan mazauna haramtattun wurare a Yammacin Kogin Jordan da Gabashin Kudus da aka mamaye.













