Gomman dubban waɗanda aka raba da gudajensu sun tsere daga North Darfur da North Kordofan sakamakon hare-haren da RSF take kaiwa, kamar yadda hukumar ba da agaji ta Sudan ta bayyana.
Da take zantawa da Anadolu ranar Lahadi, kwamishiniya Salwa Adam Benia ta bayyana cewa fararen hulan da da aka raba da gidajensu sun tsere zuwa biranen Dongola a jihar Northern State da kuma El Obeid a jihar North Kordofan.
Benia ta yi wannan kalaman ne bayan ta gana da jakadan Turkiyya Fatih Yildiz da kuma Hamza Tasdelen, mataimakin shugaban hukumar ba da gajin gaggawa ta Turkiyya (AFAD) a Port Sudan.
Godiya, Turkiyya
Ta bayyana godiya ga Turkiyya da hukumominta da ƙungiyoyin fararen hula game da yadda suka tsaya wa mutanen Sudan a lokacin wannan rikicin.
“A madadin mutanen Sudanese, ina godiya ga Turkiyya da hukumominta game da yadda suka taimaka mana a wannan lokaci mai tsananin a lokacin da muke buƙatar asalin taimako sosai.”
Benia ta ce a halin mutanen da aka raba da gidajensu dayanzu an raba mutane da yawa daga North Darfur da North Kordofan zuwa wasu birane, musamman Dongola, tana mai jaddada cewa adadinsu na ƙaruwa a ko wace rana.
Jihohi na Kordofan, jihar North da West da kuma South, sun fuskanci tsananin yaƙi tsakanin sojin Sudan da dakarun RSF a cikin ‘yan kwanakin nan.
Kwamishiniyar ta ce birnin El Obeid ya karɓi fiye da mutum 175,000 da aka raba daga muhallansu daga jihohi uku na Kordofan cikin wata ɗaya da ya gabata.
Ta bayyana cewa iyalan da aka raba da gidajensu daga Darfur da Kordofan sun kai wasu jihohi ciki har da Gadaref da Kassala a gabashin Sudan inda sama da mutum 3,000 da aka raba da gidajensu sun isa Kassala kaɗai.
Tun ranar 15 ga watan Afrilun shekarar 2023, sojin Sudan da dakarun RSF suna wani yaƙin da masu shiga tsakanin na yanki da na ƙasa da ƙasa suna gaza kawo ƙarshensa.
Rikicin ya kaseh dubban mutane tare da raba miliyoyin mutane da gidajensu



















