Shugaba Faustin-Archange Touadera ya lashe wa'adi na uku a kan mulki a JJamhuriyar Tsakiyar Afirka, bisa ga sakamakon wucin-gadi da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa ta fitar.
Hukumar ta ce Touadera ya samu kashi 76.15 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zaɓen watan jiya.
An fara zaɓarsa a shekarar 2016 kuma aka sake zaɓarsa a karo na biyu a shekarar 2020 da kashi 53.16 cikin ɗari na ƙuri'un da aka kaɗa a zagaye na farko.
Jefa kuri'ar ya biyo bayan zaɓen raba-gardama kan kundin tsarin mulki a shekarar 2023 wanda ya cire iyakance wa'adin mulkin shugaban ƙasa kuma ya tsawaita kowane wa'adi zuwa shekaru bakwai, wanda hakan ya bai wa Touadera damar tsayawa takara a karo na uku.
Tsohon malamin lissafi mai shekaru 68 ya yi kamfe ne kan abin da ya bayyana a matsayin ci gaba a fannin tsaro.
Masu sa ido na ƙasashen duniya, ciki har da Tarayyar Afirka da MINUSCA, sun bayyana zaɓen a matsayin wanda ya gudana cikin lumana, duk da ci gaba da rashin tsaro a sassan gabashin kasar.
Duk da haka, ƙawancen ‘yan adawa, Jam'iyyar RBDC, ya ƙaurace wa zaɓen, yana mai cewa ba a yi adalci ba.
'Yan takara da dama da suka shiga zaɓen, ciki har da tsoffin firaminista Anicet-Georges Dologuele da Henri-Marie Dondra, sun zargi hukumomi da sanya takunkumin yaƙin neman zaɓe, ciki har da taƙaita tafiye-tafiye zuwa yankuna da larduna.
Kotun Tsarin Mulki na da har zuwa ranar 20 ga Janairu don tabbatar da sakamakon ko yanke hukunci kan duk wani ƙalubale.
Duk da cewa 'yan adawa sun yi zargin cewa an tafka maguɗi, ya zuwa yanzu ba a bayar da rahoton wani mummunan tashin hankali bayan zaɓen ba.


















