Adadin masu zanga-zangar da suka mutu a Iran ya ƙaru zuwa mutum 4,029, in ji wata ƙungiyar kare hakkin ɗan’adam da ke da ofis a Amurka a ranar Litinin.
Jimillar mutane 26,015 aka kama ya zuwa rana ta 23 da fara zanga-zanga a faɗin ƙasar, kamar yadda alƙaluman da ƙungiyar ta tattara suka nuna.
Aƙalla mutane 5,811 sun samu manyan raunuka a yayin zanga-zangar, in ji rahoton.
Tun ƙarshen watan da ya gabata aka fara zanga-zanga a Iran, an fara daga Grand Bazaar da ke Tehran saboda karyewar darajar riyal ɗin Iran da lalacewar tattalin arziki.

Daga baya zanga-zangar ta yaɗu zuwa faɗin ƙasar.
Jami’ai sun zargi Amurka da Isra’ila da goyon bayan abin da suka kira ‘masu bore ɗauke da makamai’, waɗanda suka kai hare-hare da dama kan cibiyoyin gwamnati a faɗin ƙasar.
Shugaban Amurka Donald Trump ya sha nanata barazanar kai “mummunan hari” idan aka kashe masu zanga-zanga, amma daga baya ya ce an samu rahotannin cewa hukumomin Tehran sun soke zartar da hukuncin kisan da aka shirya aiwatarwa.




















