Abin da ya sa 'yan wasan Nijeriya mata suka fi maza lashe kofuna
WASANNI
2 minti karatu
Abin da ya sa 'yan wasan Nijeriya mata suka fi maza lashe kofunaTawagar ƙwallon kwandon da tawagar ƙwallon ƙafar ta Nijeriya suna ci gaba da shan jinjina a ciki da wajen ƙasar. Sannan Shugaban ƙasar Bola Tinubu ya karrama su da lambobin yabo da kyautar makudan kuɗaɗe.
Abin da ya sa 'yan wasan Nijeriya mata suka fi maza lashe kofuna / Others
8 Agusta 2025

A fagen wasanni, a ‘yan kwanakin nan matan Nijeriya sun kafa tarihin nuna bajintar da samun nasarorin da ake ta yi musu ayyiriri!

Idan za a tuna, a ƙarshen watan jiya ne tawagar ƙwallon ƙafa ta mata ta Nijeriya, Super Falcons ta lallasa ta ƙasar Maroko da ci 3-2 a wasan ƙarshe na cin Kofin Ƙasashen Afirka na Mata (WAFCON), wanda wannan ne ya karo na 10 da Nijeriya ta lashe wannan kofi.

Sannan a ƙarshen makon jiya ne tawagar mata ta ƙwallon kwando ta Nijeriya, wato D’Tigress ta doke takwararta ta ƙasar Mali da ci 78-64, inda Nijeriya ta zama ta farko da ta lashe kofin Gasar Kasashen Afirka ta Ƙwallon Kwando, wato AfroBasket, karo na biyar a jere.

Tawagar ƙwallon kwandon da tawagar ƙwallon ƙafar duka suna ci gaba da shan jinjina a ciki da wajen ƙasar. Sannan Shugaban Nijeriya Bola Tinubu ya karrama su da lambobin yabo da kyautar makudan kuɗaɗe.

Fifikon mata kan maza

Wannan bajintar da ’yan wasan motsa jikin Nijeriya mata suke nunawa ta sanya wasu masu sharhi kan wasanni suna cewa wataƙila gaskiya ne karin maganar nan da Turawa ke yi cewa ‘abin da maza za su iya yi, to mata ma za su iya yin sa har ma su ɗara sa’a.

Masu irin wannan magana suna kwatanta matan da takwarorinsu maza, wato tawagar ƙwallon ƙafar Nigeria, Super Eagles da kuma tawagar ƙwallon kwando ta maza ta ƙasar, wato D’Tigers.

Ga misali, sau uku kacal tawagar maza ta lashe Kofin Gasar Ƙasashen Afirka (AFCON), yayin da tawagar matan ƙasar ta lashe kofin WAFCON har sau 10.

Kazalika babu haɗi tsakanin mata da maza a ɓangaren ƙwallon kwando, inda matan suka lashe kofin AfroBasket har sau bakwai yayin da mazan sau ɗaya tak suka taba lashe kofin gasar Afirka.

Wani masanin harkokin wasanni a Nijeriyar, Malam Mansur Abubakar ya shaida wa TRT Afrika cewa ana samun wannan bambance-bambancen tsakanin maza da mata saboda a yanzu wasannin motsa jiki na mata bai bunƙasa sosai ba a nahiyar Afirka.

Ma’ana, gogayyar da ake yi tsakanin gasar mata ba ta kai ta maza ba. Masanin ya ce yanzu ne harkokin wasannin mata suka fara haɓaka a nahiyar Afirka. Kuma idan aka duba ita gasar mata ta WAFCON sai a 1991 aka fara ta, yayin da gasar maza ta AFCON aka fara ta tun a 1957.