Ministan harkokin wajen Ghana, Samuel Okudzeto Ablakwa, ya bayyana cewa ƙasar za ta karɓi ƙarin mutum 40 da za a kora daga Amurka a kwanaki kaɗan masu zuwa.
Bayanin ministan na zuwa ne bayan 'yan majalisar dokokin Ghana na jam'iyyu marasa rinjaye sun soki matakin gwamnati na karɓar mutum 14 da aka kora daga Amurka ba tare da neman izinin majalisa ba.
Sai dai kuma gwamnati ta bayyana cewa shirin karɓar mutanen an yi shi bisa yarjejeniyar fahimtar juna da ƙasar ta ƙulla da Amurka, wadda ba ta buƙatar amincewar majalisa.
Da yake magana a wani shiri na gidan talabijin ɗin Channel One ranar Laraba, Ablakwa ya tabbatar da cewa wani sabon rukuni na mutanen da aka kora daga Amurka zai isa ƙasar Ghana nan ba da jimawa ba.
“Zan iya bayyana muka cewa muna sa rai ƙarin mutum 40 za su iso Ghana nan da kwanaki kaɗan masu zuwa. Mun tantance su kafin su zo,” in ji shi.
Ya bayyana cewa Ghana ta ɗauki wannan mataki ne domin jinƙai bayan ta lura da irin mawuyacin halin da ake saka waɗanda da aka kora daga Amurka.
“Ba wai mun yarda da wannan shiri ba ne don mun amince da manufofin Shugaba. Ba wai muna yi wa Amurka wata alfarma ba ne. ‘Yan’umanmu ‘yan Afirka muke yi wa alfarma; muna ba su mafaka kuma muna so su komo gida su kasance cikin nutsuwa,” a cewar ministan.
“Mun goyi bayansu a lokacin da muka ga waɗannan hotunan na kamen da ake yi musu da kuma take haƙƙoƙinsu na bil’adama da kulle su ba tare da son ransu ba,” in ji shi..
“Mun yi shi ne kawai bisa dalilai na jinƙai; ba mu samu wani amfani na kuɗi [a kan batun] ba. Muna wannan ne domin muna son mu ci gaba da saka Ghana a matsayin ƙasar da duk ‘yan Afirka za su so zuwa,” in ji Ablakwa.