Shugaban Syria Ahmed al Sharaa ya sanar da yarjejeniyar tsagaita wuta mai cikakken iko a ranar Lahadi da SDF/YPG, wanda hakan ke nuna babban mataki na dawo da iko da arewa-maso gabashin kasar ga Damascus.
A cewar sharuɗɗan yarjejeniyar da kamfanin dillancin labarai na Syria Arab News Agency (SANA) ya wallafa, yarjejeniyar ta samar da tsagaita wuta nan-take kuma a duk faɗin ƙasar kuma a dukkan fili daga da wuraren da sojojin gwamnatin Syria da YPG ke iya haɗuwa da juna.
Yarjejeniyar ta kuma tanadi janye dukkan 'yan ta'adda masu alaƙa da YPG zuwa yankunan gabashin Tafkin Euphrates a matsayin matakin shiri na sake tura sojoji, wanda hakan zai share hanyar da gwamnatin Syria za ta sake tabbatar da iko kan yankunan da ake taƙaddama a kansu.
Yarjejeniyar ta tanadi janyewa, hade cibiyoyi waje guda, da tabbacin afuwa
A ƙarƙashin yarjejeniyar, za a miƙa lardunan Deir ez-Zor da Raqqa gaba ɗaya kuma nan-take zuwa ga gwamnatin Syria, duka a ɓangaren gudanarwa da ayyukan soja.
Duk cibiyoyin farar-hula da wuraren jama'a a lardunan biyu za a miƙa su ga hukumomin gwamnati.
Yarjejeniyar ta tabbatar da cewa ma'aikatan da ke aiki a Deir Ezzor da Raqqa za su ci gaba da kasancewa a cikin ma'aikatun gwamnatin Syria, kuma ta tanadi cewa ba za a ɗauki wani mataki na hukunci ba ga mambobin YPG ko mambobin gwamnatin farar-hula da ke aiki a yankunan ba.
A lardin Hasakah, za a haɗa dukkan cibiyoyin farar-hula cikin tsarin gudanarwa na gwamnatin Syria, wanda hakan zai ƙara faɗaɗa ikon gwamnatin tsakiya a duk faɗin arewa maso-gabas.
Yarjejeniyar ta kuma bai wa Damascus iko kan dukkan hanyoyin ketare iyaka da kuma rijiyoyin mai da iskar gas da ke yankin.
Rundunar sojojin Syria za ta tabbatar da tsaron waɗannan wurare don tabbatar da cewa an mayar da kuɗaɗen shiga ga kasar, a cewar SANA.















