Wasu da ake zargin ‘yanta’adda ne sun kai hari tare da kashe aƙalla fararen-hula 31 a wani ƙauye na yammacin Nijar da ke da iyaka da Burkina Faso da Mali, in ji majiyoyin yankin a ranar Talata.
‘Yan ta’addar da ake zargin sun kai hari ranar Lahadi a wani kauye da ke yankin Tillaberi, wanda ke yankin kan iyakoki uku - wani yanki da ke fuskantar tashin hankali inda iyakokin Nijar, Burkina Faso da Mali suka hadu waje guda.
Tsawon kusan shekaru goma, 'yanta'adda da ke da alaƙa da Al-Qaeda na kai munanan hare-hare a yankin.
"A ranar Lahadi, ‘yanbindiga ɗauke da makamai sun kashe mutane 31 daga cikin mazaunanmu a Bosiye; mutane 30 sun mutu nan take, kuma ɗaya daga cikin biyar da suka jikkata ya mutu a wata cibiyar kula da lafiya," wani mazaunin yankin ya shaida wa AFP.
'Mummunar aika-aika'
Wata ƙungiyar ɗalibai ta yankin ta kuma tabbatar da wannan adadin a cikin wata sanarwa, tana mai cewa "ta yi matuƙar mamaki da baƙin ciki" da "wannan mummunan aiki na rashin imani."
Jami'an tsaro har yanzu ba su fitar da wata sanarwa a hukumance ba har zuwa lokacin wallafa wannan labarin.
A watan Satumba, a wani harin kwanton bauna an kashe magajin garin Gorouol wanda gwamnatin riƙon ƙwarya ta Nijar ta naɗa a yankin da Bosiye yake.
Yankin Tillaberi ya zama "yanki mafi fuskanta hare-hare a tsakiyar Sahel" a shekarar 2025, a cewar ACLED, wata ƙungiya mai zaman kanta da ke sa ido kan rikice-rikice.















