Nazari kan matukan jirgin Air Peace da suka sha giya
Wani bincike na Hukumar Binciken Kan Hadurran Jiragen Sama da Sauran Ababen Hawa a Nijeriya wato Nigerian Safety Investigation Bureau (NSIB) ta gano cewa wani direban jirgin sama da mataimakinsa wadanda suke aiki da kamfanin Air Peace sun sha giya
16 Satumba 2025
Bayan hukumar ta bincike su bayan wani jirgin saman kamfanin ya kauce daga layinsa yayin da ya sauka a filin jirgin saman Port Harcourt a watan Yulin da ya gabata.
Sannan an gano wani ma’aikaci cikin ma’aikatan jirgin saman ya sha wiwi bayan da shi ma aka yi masa gwaji.