Mutum miliyan 35 za su yi fama da yunwa a 2026 – Hukumar Abinci ta MDD
Wani abu da yake kara fito da girman matsalar da take tunkarar yankin arewacin Nijeriya shi ne rahoton Hukumar Abinci ta Majalisar Dinkin Duniya (WFP) wanda ya ce kimanin mutum miliyan 35 ne za su yi fama da yunwa a shekarar 2026.
26 Nuwamba 2025
Hasashen ya ce za a fuskanci wannan matsala ce saboda yadda matsalar tsaro take ci gaba da tabarbarewa a yankin arewacin kasar da yankin Sahel, sannan dalili na biyu da hukumar ta bayar shi ne dakatar da tallafin kudin da Amurka take ba ta.