7 awanni baya
Kayode ya bayyana wa wani taron manema labarai a Abuja ranar Alhamis cewa, sun ji dadin umarnin na shugaban kasa, domin hakan zai hana mutane su matsa lambar cewa suna so a ba su masu kare su.
Ya kuma musa ikirarin da wasu kafofin labarai ke yi cewa adadin 'yan sanda ya kai 120,000, inda ya ce babu gaskiya cikin rahotannin, yana mai cewa gaba daya 'yan sandan da ke irin wannan aiki 11,566 ne kacal.

