KotunKoli ta tabbatar da nasarar Abba Kabir Yusuf a ranar Juma'a. / Hoto: AKY

Gwamnan Jihar Kano Abba Kabir Yusuf ya kafa wani kwamiti na musamman mai suna Kwamitin Dattawan Kano.

Mai magana da yawun gwamnan jihar Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya sanar da hakan inda ya ce an kafa kwamitin ne domin bayar da shawarwari ga gwamnatin jihar.

Kwamitin ya kunshi tsofaffin gwamnoni da mataimakansu da Shugabannin Majalisar Dattawa da mataimakansu.

Sauran sun hada da tsofaffin alkalan Kotun Koli da Daukaka Kara da Sakatarorin Gwamnatin Jihar da wasu manya wadanda suka rike mukamai a jihar.

Haka kuma kwamitin ya kunshi manyan malamai da ‘yan kasuwa da tsoffin shugabannin tsaro.

A cikin sanarwar, gwamnan ya gode wa Allah kan irin dattawan da Allah ya azurta jihar da su wadanda suka samu nasarori daban-daban a irin gwagwarmayar da suka yi.

Kafa wannan kwamitin na zuwa ne bayan Kotun Kolin Nijeriya ta tabbatar wa gwamnan jihar da nasara a zaben 2023 bayan a baya kotunan daukaka kara da ta sauraren kararrakin zabe sun kwace masa kujera.

A jawabin da gwamnan ya yi bayan hukuncin Kotun Koli, ya bukaci jama’ar jihar daga ciki har da ‘yan adawa da su hada hannu domin ciyar da jihar gaba.

TRT Afrika