Kotun ta yi adalci ga dukkan batutuwan da aka gabatar mata duba da hurumin doka.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu na Nijeriya ya bayyana jin daɗi da farin cikinsa tare da yin maraba da hukuncin da Kotun Koli ta yanke a kan zaben shugaban kasar, inda ta tabbatar da nasararsa.

A ranar Alhamis ne Kotun Kolin mai tawagar alkalai bakwai karkashin jagorancin Mai Shari'a John I. Okoro ta yanke hukuncin da ya zama na karshe a kan zaben shugaban Nijeriya wanda Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour ke kalubalanta.

"Kotun ta yi adalci ga dukkan batutuwan da aka gabatar mata duba da hurumin doka, ba tare da jin tsoro ko fifita wani ba, in ji Shugaba Tinubu, a sanarwar da fadarsa ta fitar jim kadan bayan hukuncin kotun.

"Babu tantama, a wannan hukunci na yau, an sake karfafawa tare da daga martabar ingancin zabe da dimokuradiyyarmu mai aiki da kundin tsarin mulki. An kuma dabbaka wannan tsarin a kimar siyasarmu saboda nutsuwa da kwarewar Mai Girma Mai Shari'ar da ya shugabanci yanke hukuncin karshe na wannan shari'a."

Shugaban na Nijeriya ya kuma ce a yayin da wannan hukunci ya kawo karshen ce-ce-ku-cen waye ya lashe zaben Shugaban kasa na 2023, kuma ya cika ka'idojin da kundin tsarin mulki ya shardanta, "Ina so na sake jaddada imanina ga tsarin shari'a na kasarmu wanda ban taba tantama game da shi ingancinsa ba.

"Saboda na san kotunanmu ba za su gaza yin adalci ga dukkan 'yan Nijeriya ba kan kowanne batu kuma a kowane lokaci.

"Yau an sake tabbatar da cewa jam'iyyata ta APC ce ta yi nasarar zabe tare da rinjayen kuri'un da 'yan Nijeriya suka jefa."

Shugaba Tinubu ya kuma ce "Tare da dimbin godiya ga Allah Mabuwayi, na karbi wannan hukunci na yau cikin ƙanƙan da kai, tare da buri da bukatar fuskantar kalubalen da ke damun al'ummarmu."

Da yake kira ga dukkan bangarori kan su zo a hada kai a gina Nijeriya, Tinubu ya ce "Dukkanmu 'yan gida daya ne, kuma wannan lokaci na bukatar mu ci gaba da aiki don gina kasarmu tare.

Karfin bambance-bambancen da ke tsakaninmu da girman kasarmu da ta hada mu waje guda, za su tirsasa mana wajen karkatar da al'ummarmu ga gina kasa mai karfi, yalwar arziki da albarka.

Ya ce "A shirye nake da na karbi duk wata gudunmawa daga kowanne dan Nijeriya don habaka cigabanmu baki daya."

Tinubu ya gode wa 'yan Nijeriya

Tinubu ya kuma mika godiyarsa ga dukkan 'yan Nijeriya bisa damar da suka ba shi na hidimtawa kasarsu.

Ya yi alkawarin zai biya bukatunsu da ma yin sama da yadda suke tsammani a bangarorin hidimtawa da tabbatar da kyakkyawan shugabanci.

Bayan zaben Shugaban Kasa a Nijeriya ne 'yan takarar jam'yyun PDP Atiku Abubakar da na LP Peter Obi suka garzaya kotun kararrakin zabe tare da kalub;antar nasarar da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bawa Tinubu.

TRT Afrika