| Hausa
AFIRKA
2 MINTI KARATU
An ga watan azumin Ramadan a Nijeriya
Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya ce ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan Nijeriya su tashi da azumi.
An ga watan azumin Ramadan a Nijeriya
Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga ƴan Nijeriya su yi wa ƙasarsu addu'a musamman game da matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa a wannan wata na Ramadana mai albarka. / Others
11 Maris 2024

Sarkin Musulmi na Nijeriya Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya sanar da ganin watan azumin Ramadana a ƙasar.

Ya bayyana haka ne a wani jawabi da ya gabatar a fadarsa da ke Sokoto ranar Lahadi, kamar yadda kwamitin ganin wata na ƙasar ya fitar.

Ya ƙara da cewar ranar Litinin za ta kasance 1 ga watan watan Ramadan, don haka ya buƙaci duka ƴan ƙasar su tashi da azumi.

Sarkin Musulmi Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III ya yi kira ga ƴan Nijeriya su yi wa ƙasarsu addu'a musamman game da matsalar rashin tsaro da tsadar rayuwa a wannan wata na Ramadana mai albarka.

Galibin ƙasashen duniya sun ga watan na Ramadana inda al'ummomin Musulman ƙasashen za su tashi da azumi.

Shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mika gaisuwar fatan alheri ga Musulman duniya a yayin da ake soma azumin watan Ramadan mai albarka.

MAJIYA:TRT Afrika