'Yan sanda a Kano sun ce za su bi umarnin kotu dangane da sha'anin sarauta a jihar.

1600 GMT — Malamai a Kano sun roƙi Tinubu kan a bar jihar ta zauna lafiya

Malamai a Jihar Kano sun fitar da sanarwa inda suka buƙaci Shugaba Tinubu ya ɗauki duk wasu matakan da suka dace domin tabbatar da zaman lafiya a jihar.

Malaman sun bayyana haka ne a wata sanarwa da suka fitar su 18 a ranar Asabar.

Malaman sun jaddada cewa yanayin da ake ciki dangane da batun rikicin masarautu a jihar, idan ba a bi abubuwa a hankali ba, lamarin zai iya zama wani babban rikici.

Malaman sun buƙaci shugaban ƙasar da ya bar Kanawan sun magance matsalarsu ta cikin gida ba tare da an yi amfani da ƙarfi ba.

1131 GMT Sarki Muhammadu Sanusi II ya yi zaman fada

A karon farko bayan ya koma kan karagar mulki, Sarki Muhammadu Sanusi ya yi zaman fada da safiyar Asabar.

Sarkin ya hau doki daga cikin gida zuwa fada domin zaman, inda mutane ke binsa suna sowa da nuna goyon bayansu a gare shi.

Wasu daga cikin hakimai na Kano sun je sun miƙa gaisuwa ga sarkin.

Wannan na zuwa ne a yayin da ake zaman ɗar-ɗar inda ake tunanin Aminu Ado Bayero zai koma fadar ta Kano tare da rakiyar jami’an tsaro.

Sarkin ya yi zaman fadar ne yayin da ake ci gaba kan dambarwar sarauta a jihar. / Hoto: Others

1054 GMT — Shugabannin tsaro na Kano sun ziyarci Aminu Ado Bayero

Manyan jami’an tsaro daga ciki har da kwamishinan ‘yan sanda da na DSS da soji reshen Kano sun ziyarci Alhaji Aminu Ado Bayero a Nasarawa.

Wannan na zuwa ne bayan taron manema labarai da gwamnan jihar ya yi da safiyar yau Asabar.

A baya dai gwamnan na Kano Abba Kabir Yusuf ya bayar da umarnin a kama Aminu Ado Bayero, sai dai kwamishinan ‘yan sandan Usaini Gumel ya ce ba su samu wannan umarnin a hukumance ba.

Ana ci gaba da dambarwar sarauta a Kano. / Hoto: Others

1030 GMT Za mu bi umarnin kotu dangane da sha'anin masarautu a Kano — 'Yan sanda

Kwamishinan ‘yan sandan Kano Mohammed Usaini Gumel ya bayyana cewa za su yi wa umarnin da Kotun Tarayyar Nijeriya ta bayar biyayya dangane da rikicin masarautu a Kano har sai kotun ta yi zama.

Ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai wanda aka gudanar da safiyar Asabar a Kano.

Ya bayyana cewa ba za su amince da tayar da tarzoma a jihar ba inda ya ce za su yi duk mai yiwuwa domin tabbatar da zaman lafiya.

Ko da aka tambaye shi danagane da batun halin da ake ciki da dangane da masarautu a jihar sai ya ce "za mu bi umarnin kotu, wadda ta ce a bar abubuwa yadda suke. Ana nufin masarautu su koma yadda suke a baya har zuwa ranar hudu ga watan Yuni," in ji kwamishinan.

1015 GMT Bayani a taƙaice kan abin da ke faruwa

A cikin makon nan ne Majalisar Dokokin Kano ta yi doka inda ta rushe masarautun jihar biyar waɗanda gwamnatin baya ta samar.

Bayan haka ne gwamnatin Kano ƙarƙashin Abba Kabir Yusuf ta naɗa Muhammadu Sanusi II a matsayin sabon Sarkin Kano a ranar Juma'a.

Sai dai ranar Juma'a da tsakiyar dare ne Alhaji Aminu Ado Bayero ya sauka a filin jirgin sama na Malam Aminu da ke Kano, daga nan ya zarce Gidan Sarki na Nasarawa, wanda ke da nisan kimanin kilomita ɗaya daga Gidan Gwamnatin Jihar Kano.

Wannan dalili ne ya sa jama'a suka soma zargin cewa yana so ya koma kan kujerarsa ta sarauta.

TRT Afrika