Kungiyar Musulmai ta yi Allah wadai da 'makircin' Isra'ila kan Falasdinawa

Kungiyar Musulmai ta yi Allah wadai da 'makircin' Isra'ila kan Falasdinawa

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya da ta kwato wa Falasdinawa hakkinsu
Shugaban kungiyar Izala ta Nijeriya, Seikh Abdullahi Bala Lau ya bukaci masu hanu da shuni su agaza wa Falasdinawa:Hoto/Facebook/JIBWIS

Kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Iqamatis Sunnah da ke Nijeriya ta yi Allaha yi kira ga Majalisar Dinkin Duniya "ta dauki mataki kan zaluncin" da Isra'ila take yi wa Falasdinawa.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a shafinta na Facebook ta ambato shugabanta Sheikh Abdullahi Bala Lau yana cewa ya kamata a bai wa Falasdinawa hakkinsu a lokacin da yake magana a wa'azin kasa da kungiyar ta gudanar a jihar Katsina a arewa maso yammacin Nijeriya.

Shugaban ya ce Isra'ila tana kauce wa duk wani kudurin zaman lafiya da ake kawowa Majalisar Dinkin Duniya.

Ya kara da cewa Majalisar Dinkin Duniya ba ta da amfani idan ba za ta iya kwato wa Falasdinawa hakkinsu ba.

Sheikh Bala Lau ya yi kira ga al'ummar Musulmai da su yi addu'a Allah ya yi maganin masu zaluntar Falasdinawa.

TRT Afrika