Ma'aikata a Nijeriya sun koka dangane da halin matsin rayuwa da suke ciki a ƙasar.

Ma'aikatan Nijeriya sun bayyana matuƙar ɓacin ransu game da tsadar rayuwa sakamakon tashin farashin kayan abinci da sauran kayayyaki bayan gwamnati ta janye tallafin man fetur a yayin da ake bikin Ranar Ma'aikata ta 2024.

Hakan na faruwa ne a yayin da harkokin sufuri da na kasuwanci a manyan biranen ƙasar suka fuskanci tsaiko sakamakon ƙarancin fetur da ya haddasa dogayen layuka a gidajen mai.

Garba Rabiu Kura, wani ma'aikaci a jihar Kano da ke arewacin ƙasar, yai shaida wa TRT Afrika cewa tashin farashin kayayyaki ya sa albashinsu ba ya iya kai su ko da kwana goma.

Ya ce, "Tun da gwamnati ta janye tallafin man fetur a shekarar da ta wuce albashinmu ya zama tamkar babu shi. Da ma can ba wani abun kirki yake tsinana mana ba, amma yanzu lamarin ya yi ƙaramin da ba zai iya saya wa mutum buhun shinkafa ba. Ka ga ba a maganar sauran abubuwan da za a haɗa shinkafar da su," in ji shi.

Shi ma Frank Ajayi, wani ma'aikaci a birnin Ibadan na jihar Oyo, ya shaida wa TRT Afrika tsadar rayuwa ta sa ba sa iya ajiye komai a cikin albashinsu.

“Zai yi matuƙar wahala ma'aikaci ya ajiye wani abu. Ƙarancin man fetur da ake fuskanta a koyaushe ya sa ana yawan ƙara kuɗin mota, lamarin da kan yi tasiri kan farashin kayan abinci. Duk yawan albashinka zai ƙare kafin ƙarshen wata," a cewarsa.

Ƙwarewa a wurin aiki

Ruth Oga, wadda ke aiki a matsayin jami'ar kula da ma'aikata a Legas, ta shaida wa TRT Afrika cewa ƙaruwar hauhawar farashi na tasiri matuƙa wurin ɗaukar aiki sakamakon masu kamfanoni na gwagwarmaya wurin biyan albashi.

"Kamfanoni da dama na ƙin ɗaukar aiki sakamakon a halin yanzu sun fi mayar da hankali ta ɓangaren kula da ma'aikatan da suke da su a halin yanzu, inda suke ƙoƙarin biyan albashinsu a duk wata saboda hauhawar farashi."

Ƙungiyoyin ma'aikata da dama a Nijeriya sun nuna damuwarsu dangane matsin tattalin arziƙin da ake fama da shi inda suke kokawa kan ƙaruwar farashin abinci wanda yake sakawa suna shan wahala kafin biyan buƙatunsu.

A watan Maris, hauhawar farashi a Nijeriya ya ƙaru zuwa kaso 31.70 cikin 100 a maimakon 29.90 cikin 100 wanda aka samu a Janairu, kamar yadda bayanai daga Hukumar Ƙididdiga ta Nijeriya ta fitar.

Ƙarin albashi

A ranar Talata, Gwamnatin Tarayyar Nijeriya ta sanar da cewa ta yi ƙarin albashi ga ma'aikatan gwamnati tsakanin kaso 25 cikin 100 zuwa 35, inda za a sa ya soma aiki tun daga watan Janairu.

Ƙaramin ma'aikaci na gwamnati ana biyansa naira 450, 000 a duk shekara, kimanin $323.97, wanda hakan ke nufin yana samun aƙalla 37,500 a duk wata, kamar yadda hukumar kula da albashin ma'aikata ta Nijeriya ta tabbatar.

Wannan ƙarin ya shafi duka ma'aikatan gwamnatin tarayya, daga ciki har da ma'aiktan lafiya da ilimi da jami'an tsaro.

TRT Afrika