Yara da matasa suna amfani da tashe don barkwanci. / Hoto: TRT Afrika      

Daga Abdulwasiu Hassan

Tashe dadaddiyar al’ada ce ta wasan kwaikwayo tsakanin al’ummar Hausawa a yammacin Afirka, wadda ke nuna yadda Musulmai suke debe kewa lokacin azumin watan Ramadana.

Yara sukan hadu su yi shiga ta daban, da kwalliya don kwaikwayo, suna zagaya layuka da kasuwanni da yamma ko bayan bude-baki.

Yaran sukan samar da nishadi lokacin ibadar azumi, kuma suna samun kudi ko wata kyauta. Yara mata da maza suna yin tashe, amma ba a tare ba.

Wannan al’ada ta gabaci zuwan Musulunci kasar Hausa. A yanzu tana fuskantar kalubale kamar haramci daga gwamnatoci.

Muhammad Tahar Adam, malami a tsangayar harsunan Nijeriya ta Jami’ar Bayero ta Kano ya ce, “A wancan zamanin lokacin da aka kai kayan gona gida, yara suna yin wasanni a gidajen manyan manoma.”

Mata ma suna yin tashe. / Hoto: TRT Afrika

Malam Adam ya fada wa TRT Afrika cewa, “Maza suna nasu a waje, inda mata ke yi cikin gida”.

“Sai dai bayan zuwan Musulunci, an mayar da lokacin tashe zuwa watan azumi, bayan sha ruwa. Mutane suna taruwa a gaban gidajensu, ko a dandali, ko fada”.

Salon Tashe

Duk da cewa babban jigon wasan Tashe shi ne isar da sako ko nishadartarwa, salon wasannin ya bambanta tsakanin al’ummomi.

Wasannin tashe suna fadakarwa kan batutuwa kamar tarbiyya, kula da tsofaffi, taimaka wa marasa galihu da kuma kiwon lafiya.

Wani salon tashe da ya yi suna shi ne na kula da dattijai, mai taken “Tsoho da gemu”. Akan samu yaro da zai yi shigar tsoho yana rankwafa da sanda a hannunsa.

Malam Muhammad Tahar Adam ya bayyana cewa, masu tashen za su yawata cikin gari suna waka suna neman mutane su saurare su.

Akwai wani nau’in tashe da ke fadakarwa kan zaluntar iyalai da matan aure.

Tashe da zamani

Sauyin zamani ya saka tashe ya dauki sabon salo don dace wa da zamani.

An shigo da salon tashe da ke da sabon jigo, kamar na siyasa.

A cewar Malam Muhammad Tahar Adam, “Akwai wani tashe game da wani dan majalisa, wanda ke nuna cewa ya saci kudi”.

Sai dai hukumomin sun haramta wannan tashen don gudun kar a bata sunan ‘yan majalisa.

Matasa suna sake salon tashe duk da kalubalen da yake fuskanta. / Hoto: TRT Afrika

Da alama wannan sauyin zamani shi zai taimaka wajen rike al’adar ta tashe. Wasannin tashe sun bambanta tsakanin al’ummomin Hausawa mazauna yankuna mabambanta.

“Don haka tashe al’ada ce ta Hausawa, amma akwai tashe kala-kala da ake kirkira.''

TRT Afrika