Kirkirarriyar basira (AI) tana "kirkirar mawakiya" da ake kira Mya Blue. Hoto: Reuters

Salon kade-kade na Afrobeats daga Legas yana samun karbuwa ga miliyoyin mutane kuma ya sa an sake tunani kan yadda ake kallon kade-kaden Afirka. Yana ci gaba da samun karbuwa a duniya, inda ake ci gaba da samun mawaka da ke kwaikwayonsa.

Lokacin da manhajar kirkirarriyar basira (AI) ta fara yaduwa a fannin kade-kade a Nijeriya, Eclipse Nkasi ya yi zaton cewa abincinsa ya kare a matsayinsa na mai shirya wakoki.

Daga nan sai ya ja baya, sai ya fahimci akwai damarmaki da 'yan matsaloli, kuma sai ya yi amfani da fasaha wajen samar da wani sabon salon album din Afrobeats a studiyonsa a wajen birnin Legas.

"Babu bukatar kirkirarriyar basira ta maye gurbin abin da muke da shi.

Tana ba mutane sabon abu… kuma ta wannan fuskar ce nake ganin na yi amannar kirkirarriyar basira za ta sauya abubuwa," kamar yadda Nkasi ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A baya, sai ya kashe dubban daloli kuma za a kwashe tsawon wata uku wajen shirya wakokin, daukar mawakan da daukar bidiyon wakar da zama a tsara a studiyo da kuma a kaarshe fitar da wakar ga masu sha'awa.

Kwamfuta tana rubuta wakar da kanta

Wannan ana bukatar kwana uku da dala 500.

Nkasi da abokansa uku sun koma amfani da manhajar kirkirarriyar basira ta ChatGPT kuma suna amfani da ita wajen shirya wakoki tara a album da ake kira "infinite Echoes".

Eclipse Nkasi ya gyara murya da salon wakar ta hanyar amfani da kirkirarriyar basira.

Suna sa kirkirarriyar basira ta samar da rubutun waka da kuma sunanta – ciki har da wakoki kamar "God Whispers" da "Love Tempo" da kuma "Dream Chaser".

Daga nan sai su gyara kalmomin da kansu don su dace da maudu'insu – wannan ce fafutikar mawaki wanda ba ya so ya yi watsi da shaukinsa na kirkirar waka.

Daga nan kuma sai su yi amfani da wata kirkirarriyar basira wajen fitar da amo. Nkasi yana nadar wasu muryoyi kuma sai ya dora su kan wata manhaja – wacce take sauya muryoyin zuwa muryar da aka kirkiro saboda album din.

Wannan mawakiyar da aka kirkiro da ake kira Mya Blue wadda ta bayyana a gaban 'yan kallo a intanet a matsayin katun din kwamfuta.

Sauya salon mawaka

"Akwai abubuwa da za su zama an daina yayinsu saboda kirkirarriyar basira," in ji Nkasi. Amma kuma za ta samar da damarmaki ga mawaka wajen sauya salonsu da gyara aikinsu da yin aikin cikin sauri, a cewarsa.

Fasahar har ta fara sauya masana'antar kuma za ta yi tasiri mai kyau kan ingancin abin da ake samarwa da yadda ake nadar wakokin, a cewar wani mai sharhi kan wakoki da ke zaune a Legas Omotolani Alake.

Kodayake akwai wasu bangarori da ba a da tabbas, ciki har da fannin hakkin mallaka, da ya kamata a yi la'akari da shi da kuma bunkasa shi," in ji shi. "Muna a farko-farko ne."

TRT Afrika da abokan hulda