| Hausa
KASUWANCI
2 MINTI KARATU
Hare-haren sama na sojin Nijeriya sun lalata matatun man da ke aiki ba bisa ka'ida ba
An kai harin saman ne kan wasu wurare shida a jihar Ribas da aka tabbatar da cewa ana satar man fetur a wajen, in ji rundunar sojin.
Hare-haren sama na sojin Nijeriya sun lalata matatun man da ke aiki ba bisa ka'ida ba
An tabbatar da cewa ana gina matatun mai na wucin gadi a yankunan. Hoto:  Nigeria Airforce / Others
26 Disamba 2023

Sojojin Najeriya sun lalata haramtattun matatun mai a yankin Neja Delta da ke kudancin kasar a kokarin da suke yi na kai hare-hare kan barayin mai da masu fasa bututan mai, in ji rundunar a ranar Talata.

An lalata wasu gine-ginen da ɓarayin mai ke amfani da su wajen sarrafa danyen mai zuwa tataccen fetur da ake sayarwa.

An kai harin saman ne wasu wurare shida da aka tabbatar da cewa ana satar mai ne, in ji kakakin rundunar sojin saman Nijeriya Edward Gabkwet a wata sanarwa da ya fitar.

Ya ce, “Ana ci gaba da ayyukan samame da jiragen sama na yaki kan masu aikata laifuka a yankin Neja-Delta da sauran sassan kasar ba ƙaƙƙautawa."

Satar fetur ya zama ruwan dare

Samar da matatun mai ba bisa ka'ida ba ya zama ruwan dare a Nijeriya - daya daga cikin manyan kasashen Afirka da suka fi samar da fetur din.

Kakakin ya ƙara da cewa, shugaban rundunar sojin saman Nijeriya Air Marshal Hassan Abubaka, ya yaba wa kokarin.

Masu amfani da matatun fetur ba bisa ka'ida ba sun kasance suna satar mai daga bututan mai da kamfanoni ke sarrafawa.

Nijeriya dai na da kusan ganga biliyan 37 na arzikin danyen mai da aka tabbatar, a cewar kungiyar kasashe masu arzikin man fetur ta Opec.

MAJIYA:TRT Afrika