Manyan kamfanonin zuba jari na Amurka Pimco da Vanguard sun sayi kadarori a Turkiyya a 'yan watannin nan, in ji manyan shugabannin zartarwar kamfanonin, suna masu cewa kasar za ta ci gaba da aiki da manufofin habakar tattalin arziki masu karfi.
Shugabannin zartarwar manyan kamfanonin biyu mafi yawan zuba jari a duniya da suke da kadarorin kusan dala tiriiyan $2, sun nuna yarda da Turkiyya, saboda ta rungumi sabbin manufofin ci-gaban tattalin arziki, da suka hada da kara yawan kudin ruwa a watan Yuni, bayan nasarar zabe da Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya yi.
Pimco da Vanguard Pimco da Vanguard ba su bayyana takamaiman yawan kadarorin da suka saya ba, amma zuba jarinsu alama ce ta amincewa da kasuwannin Turkiyya.
"Mun yanke hukuncin sayen kadarori a Turkiyya, musamman kadarorin kudin kasar, saboda tsauraran sharuddan ta'ammali da kudade don magance hauhawar farashi, da kuma saukaka ka'idojin da ke lalata darajar kadarorin," in ji Pramol Dhawan, manajan darakta na kamfanin Pimco da ke kadarori na kusan dala tiriliyan $2.
Masu zuba jari na kwararo wa
Vanguard, kamfani na biyu mafi girma a duniya da ke juya kudade da ya mallaki kadarori na kusan dala tiriliyan 7.5 ya sayi kadarori a Turkiyya ba tare da wani dardar ba a karshen shekarar da ta gabata, bayan da Nick Eisinger, shugaban sashen kasuwa na kamfanin tare da wasu masu zuba jari sun ziyarci kasar.
A watan da ya gabata an samu nuna sha'awar zuba jari a Turkiyya daga kasashen waje mafi yawa a cikin shekaru shidan da suka gabata, inda matakin musayar basussuka (CDS), muhimman ma'aunin kasada, ya sauko zuwa kasa da matakin rabi a watan Mayu.
A watan Yuni, Shugaba Erdogan ya sanar da sunayen sabbin ministoci da shugabar babban banki Hafize Gaye Erkan, wadda tuni ta kara yawan kudin ruwa da maki 3,400 zuwa kashi 42.5.
Bankin ya bayyana cewa, matakin zai dakatar da hauhawar farashi ba da jimawa ba, amma ya sake tsaurara dokokin da manufofin sarrafa kudade
Mahukunta na kuma aiki don saukaka dokoki, ta yadda za a kubutar da kasuwannin ta'ammalin kudade.
Sabon shafi
Bayan sake zabar sa a watan Mayu, Shugaba Erdogan ya kawo sabbin jam'ian tattalin arziki, wadanda suke tsananta aiki da dokokin sha'anin kudade, a yayin da babban bankin Turkiyya ya kara yawan kudin ruwa daga kashi 8.5 zuwa kashi 42.5.
Bayan nada Mehmet Simsek a matsayin Ministan Kudi da Baitulmali bayan zaben watan Mayu, an samu muhimman sauye-sauye a fannin kudade a Turkiyya.
SImsek ya bayyana saukar da farashi, tsantsanin kashe kudade, da sauye-sauye a matsayin manyan ginshikan shirin habaka tattalin arziki na Turkiyya a matsakaicin zango, tsakanin 2024 da 2026.
Wannan sauyi ya sanya kudaden Babban Bankin a ma'ajiyar kasashen waje ya karu zuwa dala biliyan $142.53 a ranar 15 ga Dismaba, inda bankin ya bayyana karuwar dala biliyan $1.15 sama da adadin makon da ya gabata.