Cibiyar Nadar Wakoki ta sanar cewa mai wasan barkwanci dan Afirka ta Kudu, Trevor Noah ne zai zama mai gabatarwa a wajen bikin GRAMMY na 2025. Wannan ne karo na biyar a jere da yake kasancewa mai gabatar da baki da shirye-shiryen Bikin Wakoki Mafi Girma.
'The GRAMMYs' da aka fi sani da 'Grammy Award" Kambin Grammy', bikin bayar da kambi ga mawaka da 'Recording Academy' ke daukar nauyi, ind ake zabar mawakan da suka fi yin fice.
"Cibiyar 'Recording Academy' da CBS ta sanar da cewa mai wasan barkwancin da ya shiga takarar lashe kambin Grammy kuma ya lashe kambin Emmy, kuma marubuci Trevor Noah zai sake dawowa a matsayin mai gabatarwa a bikin 2025. Noah zai kuma yi aiki a matsayin mai yin shiri a wajen," in ji shafin yanar gizon wadanda suka shirya bikin.
An haife shi a Johannesburg, Afirka ta Kudu, Trevor Noah ya fara wasan barkwanci bayan kawo karshen mulkin nuna wariya na tsiraru bakar fata a Afirka t Kudu, kuma yana yin barkwanci da gabatar da shirye-shiryen talabijin daban-daban. Ya samu karbuwa a matakin kasa da kasa a matsayin mai gabatar da 'The Daily Show' , wani shirin Amurka na barkwanci da zambo a tsakanin 2015 da 2022.
Ya lashe kambi da dama
Noah mawakin barkwanci da ya taba lashe gasar Emmy, kuma a yanzu yake takarar lashe kambin GRAMMY, marubuci ne, mai shirya wakoki, inda ya lashe kambin shirya shirye-shirye mafi kayatarwa a gasar 'EMMY Awards' karo na 75 a watan Janairun 2024.
Mahukuntan 'The Grammys' sun bayyana kaifin basirar Noah, kwarjini, da tunani na musamman a matsayin abubuwan da suka sanya shi zama "wanda ake kauna a masana'antar nishadantarwa"
Ayyukansa na baya
Trevor Noah ya assasa sunansa a wasannin ban dariya da tsari mai kyau a wajen shirye-shiryen GRAMMY tun shkarar 2021.
2021 GRAMMYs: Shekarar farko da Noah ya fara gabatarwa a taron GRAMMYs, wanda a lokacin ana fama da COVID-19 hakan ya sanya aka yi taron sadarwar yanar gizo. Ya nuna basira da kwarewa a taron na yanar gizo, inda ya nishadantar da mahalartan a tsawon daren.
2022 GRAMMYs: Noah ya dawo fage a shekara ta biyu a matsayin mai gabatarwa da ya kawo daidaito ga bikin bayan annobar. Ya tabo batutuwa irin su COVID-19, adalcin zamantakewa, a yayin da yake kuma nishadantar da mahalarta da masu kallo.
Shekarar Noah ta uku a matsayin mai gabatarwa ta ba shi damar bayyana kwarewar da basirarsa wajen tabo batutuwa daban-daban wanda masu nazari a wannan lokaci suka ce sun taimaka wajen inganta auna shirye-shiryen talabijin wanda ya sha fama da alkaluma kwan gaba kwan baya.
2024 GRAMMYs: Shekara ta hudu ta Noah a matsayin mai gabatar da shiri ta samu halartar mawaka da dama mashahurai. Wata gaba mai muhimmanci ita ce irin bayaninsa da ya yi don nuna muhimmancin yin bikin raya al'adu mabambanta.
Za a gudanar da bikin 2025 GRAMMYs a ranar Lahadi, 2 ga Fabrairun 2025, a Dandalin Arena na Los Angeles. Masu shirya bikin sun ce taron na wannan shekarar na da manufa ta musamman, tare da karin kokari na taimaka wa wadand agobarar daji ta rutsa da su, sannan a girmama kokarin farko na masu mutanen da suka kai agaji.
'The Recording Academy' sun yi alkawarin dala miliyan daya don tallafa wa masu ruwa da tsaki a masana'antar kade-kade da raye-raye da suka yi tasiri wajen kashe gobarar daji da ta afku a Los Angeles.