Kano ita ce jihar da ta fi yawan jama’a a Arewacin Nijeriya. Hoto/ Facebook/ Sanusi Bature

Daga Abdulwasiu Hassan

A tsakiyar watan Oktoba ne a Babban Masallacin Kano, inda dubban Musulmai suke zuwa don yin sallar Juma’a a kowane mako, ya karbi bakuncin auren gayya da gwamnatin jihar ta dauki nauyi.

Rana ce ta musamman ga da yawa daga cikin masallatan – maza sanye da kaya iri daya wato farar doguwar riga da jar hula.

Suna cikin angwayen da gwamnatin jihar Kano ta aurar da su 1,800 kowanne da amaryarsa.

Gwamnatin jihar Kano ta fara shirin aurar da wasu ’yan jihar ne a shekarar 2012 don taimaka wa zawarawa da matan da mazajensu suka rasu da marasa karfi wadanda ba za su iya daukar nauyin aurensu ba.

Yana daya daga cikin shirye-shiryen gwamnati don raya sunnar aure da kuma magance “badala” a cikin al’umma.

Bikin auren da aka yi na baya bayan nan shi ne na ranar 13 ga Oktoban shekarar 2023.

An daura auren gayya ne a ranar 13 ga watan Oktoba 2023. Hoto/ Facebook / Sanusi Bature

"Ina alfahari da wannan gagarumin bikin aure. Ya sanya gamsuwa da farin ciki a raina fiye da yadda kuke tunani,” kamar yadda Ahmad Saleh, daya daga cikin wadanda suka ci gajiyar shirin ya shaida wa TRT Afrika.

Kano, ita ce jiha mafi yawan al'umma a arewacin Nijeriya kuma tana cikin jihohi goma sha biyu a arewacin kasar da ake bin tsarin Shari'a Musulunci karkashin tanadin dokokin kasar.

Gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf, ya ce gwamnati ce ke daukar nauyin daurin auren domin a taimaka wa talakawa a cikin al’umma don su yi aure.

An bai wa sabbin amaren kyautuka na kayayyakin gida da tsabar kudi don su ja jari a gidajen su na aure.Photo/Facebook/Sanusi Bature

Gwamnati ce ta bayar da sadaki da kayayyakin gida da kuma jari ga kowane ma'aurata - don ba su damar fara kasuwanci da nufin tallafa wa kawunansu.

"Wata hanya ce ta tallafa wa mutane ta fuskar tattalin arziki," a cewar Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, shugaban kwamitin Hisbah na jihar da ke kula da shirin auren gata, a hirarsa da TRT Afrika.

Sheikh Daurawa ya ce shirin na taimakawa wajen rage yawan mutuwar aure a jihar.

"Na gode wa gwamnatin jihar bisa wannan karamci," in ji Ahmad wanda ya kasance daya daga cikin wadanda suka karbi kyaututukan da aka tanada a sabon shirin, cikin murmushi.

Shirin na kara habaka tun bayan bullo da shi sama da shekaru goma da suka gabata. Ya zuwa yanzu sama da ma’aurata 6,500 ne suka ci gajiyar shirin a jihar Kano da ma wasu jihohi da dama na yankin, sannan an samu wasu jihohi da suka yi koyi da shi a cikin shekarun.

Jihohin da suka yi koyi da irin wannan shiri sun hada da jihar Gombe da Sokoto da Kaduna – duk da cewa nasu bai kai girman na jihar Kano ba.

An bai wa ko wacce Amarya tsabar kudi N20,000 a matsayin jari:Photo/Facebook/Sanusi Bature

Bayan daura auren, gwamnatin jihar ta shirya gagarumar liyafa domin taya sabbin ma'auratan murnar aurensu inda ta gayyato manyan baki daga wurare dama a ciki da wajen kasar.

Wannan wata dama ce ga malaman addinin Musulunci na yin wa'azi ga sabbin ma'aurata da kuma al'umma baki daya kan ni'imomin aure da albarkar da ke cikinsa da kuma kiyaye ka'idojin koyarwa addinin Musulunci kan iyali.

TRT Afrika