| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Harbin bindiga ya raunata wata mata a gaban ofishin jakadancin Sweden na Izmir a Turkiyya
Matar, wacce ta ji mummunan rauni, tana aiki ne a Ofishin jakadancin Sweden da ke lardin Izmir, kuma a halin da ake ciki tana cikin mawuyacin yanayi, kana an ce mutumin da ya harbe ta yana fama da matsalar kwakwalwa.
Harbin bindiga ya raunata wata mata a gaban ofishin jakadancin Sweden na Izmir a Turkiyya
Ofishin gwamnan yankin ya ce wanda ya kai harin yana fama da matsalar kwakwalwa. Hoto: AA / Others
2 Agusta 2023

Wata ma'aikaciya 'yar kasar Turkiyya ta samu munanan raunuka sakamakon harin da aka kai a gaban ofishin jakadancin Sweden a lardin Izmir da ke yammacin kasar.

An kai harin ne a wajen karamin ofishin jakadancin Sweden, kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito.

Matar dai tana aiki ne a matsayin sakatariya a ofishin diflomasiyyar, kuma tana cikin mummunan yanayi, a cewar rahotanni.

Ofishin gwamnan yankin ya ce wani “mai fama da matsalar kwakwalwa ne” dan kasar Turkiyya ya kai harin a gundumar Konak da misalin karfe 09:45 agogon GMT.

"Jami'an hukumar bayar da agajin gaggawa mai lamba 112 ne suka kai majinyaciyar 'yar asalin Turkiyya asibitin horo da bincike na Tepecik don ba ta kulawa," a cewar sanarwar Ofishin gwamnan Izmir.

“An mika wanda ya (aikata laifin) ga jami'an tsaronmu tare da makamin da ya yi amfani da shi, kuma za a ci gaba da bincike kan lamarin”.

Ministan shari'a na Turkiyya Yilmaz Tunc ya yi Allah wadai da harin inda ya kara da cewa "an fara gudanar da bincike game da wannan mummunan lamari".

Ma'aikatar harkokin wajen Sweden ta ce tana kan tuntubar babban ofishin jakadancinta da ke Istanbul, bayan harin da aka kai.

Kananan ofisoshin jakadanci suna wakiltar bukatun 'yan kasarsu ne a waje amma ba kwararrun jami'an diflomasiyya ke tafiyar da ayyukansu ba.

MAJIYA:TRT World