| Hausa
TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Trump ya jaddada abotarsa da Erdogan yayin da yake magana game da Syria
"Idan ka dubi abin da ya faru a Syria, Rasha ta raunana, Iran ta raunana. Kuma mutum ne mai wayo sosai," in ji Trump game da Erdogan.
Trump ya jaddada abotarsa da Erdogan yayin da yake magana game da Syria
Goyon bayan da Washington ta bai wa ƙungiyar SDF inda YPG ke da rinjaye a Syria ya kasance babban batun sa-in-sa tsakanin Turkiyya da Amurka. / Hoto: AP / Others
8 Janairu 2025

Zaɓaɓɓen shugaban Amurka Donald Trump ya jaddadada cewa Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan wani “aboki” ne da yake girmamawa.

Bayanansa sun fito ne a lokacin da aka tambaye shi game da yiwuwar janye dakarun Amurka daga Syria da zarar ya hau karagar mulki a cikin wannan watan a wani taron manema labarai a gidansa da ke Mar-a-Lago a Florida ranar Talata.

“Ba zan ce maka komai a kan wannan ba, saboda yana cikin dabarun soji, amma zan ce Turkiyya ce,” in ji Trump. “Shugaba Erdogan abokina ne. Mutum ne da nake so, nake girmamawa. Ina ganin shi ma yana girmama ni.”

“Amma idan ka kalli abin da ya faru a Syria, Rasha ta yi rauni, Iran ta yi rauni. Kuma shi mutum ne mai wayo, kuma ya tura mutanensa can ciki ta hanyoyi daban-daban, kuma sun karɓi iko,” a cewar Trump.

A watan da ya gabata ne dai gwamnatin Bashar al Assad ta faɗi bayan gamayayyar ‘yan adawa sun ƙwace iko da muhimman biranen Syria cikin sauri.

Miliyoyin ‘yan Syria, ciki har da shugabannin ‘yan adawa, sun koma Turkiyya domin tserewa daga uƙubar gwamnatin Assad. Wasunsu sun koma domin gina ƙasarsu da yaƙi ya lalata.

Amurka na da kimanin dakaru 2,000 a Syria, inda Washington ta daɗe tana neman halasta kasancewar ƙungiyar ta’addanci ta PKK da kuma reshenta na Syria, YPG, da sunan yaƙi da Daesh.

Kawo yanzu dai goyon bayan Washington ga ƙungiyar SDF inda YPG ke da rinjaye ya kasance wani muhimmin batun sa-in-sa tsakanin Tuirkiyya da Amurka.

MAJIYA:TRT World