Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdoğan ya yi karin haske kan harin da Isra'ila ke kaiwa Gaza a taron kungiyar tsaro ta NATO da ke gudana a birnin Washington DC. / Hoto: AFP

Taron kolin kungiyar tsaro ta NATO da ke gudana a birnin Washington ya zama wani muhimmin taro a yayin da ake tsaka da fama da manyan tashe-tashen hankula guda biyu: yayin Ukraine da na Gaza da aka yi wa awanya.

A yayin da shugabannin kasashe mambobin kungiyar ke tattaunawa kan muhimmin goyon baya ga Ukraine, taron na kunshe da batutuwan hadin kai da tashin hankali.

Shugaban Amurka Joe Biden, wanda ya karbi bakuncin taron, ya jaddada jajircewar kungiyar tsaro ta NATO game da tsaron kasar Ukraine.

"Mun tsaya tare a kan ƙudurinmu," in ji shi, yana mai jaddada hadin kan kungiyar.

Amma duk da haka, a yayain da ake tattaunawa kan Ukraine, rikicin Gaza ya yi ƙamari, wanda shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya gabatar da batun.

"A yayin taron shugabannin kungiyar tsaro ta NATO, za mu yi tsokaci kan kisan kiyashin da ake yi wa al'ummar Falasdinu a Gaza, inda ake yin gwaji na gaskiya kan kyawawan dabi'unmu," in ji Shugaba Erdogan gabanin taron.

"Al'ummomin kasa da kasa sun kasa hana Isra'ila, kuma tsarguwa ba za ta bari mu samu nutsuwa ba har sai an samar da zaman lafiya mai ɗorewa a Falasdinu."

A ranar Laraba, Shugaba Erdogan ya gana da Shugaban Gwamnatin Jamus Olaf Scholz inda suka tattauna kan hare-haren da Isra'ila ke kai wa Gaza.

Shugaban na Turkiyya ya nuna wa Scholz muhimmancin matsa wa Isra'ila lamba ta dakatar da kai hare-hare a Gaza da kuma amfani da damar da ta samu na tsagaita wuta, kamar yadda hukumar sadarwa ta Turkiyya ta ruwaito.

Ya kuma jaddada bukatar ƙara zage damtse wajen daƙile ɓarkewar rikici a yankin.

Tun da farko, Erdogan ya gana da firaministan kasar Girka Kyriakos Mitsotakis, inda ya nanata saƙon cewa, ya kamata a ƙara ƙoƙari wajen kawo ƙarshen rikice-rikicen da ke faruwa a Falastinu da Ukraine.

Tattauna batun tsagaita wuta a Gaza

Muhimmancin da Turkiyya ke da shi na yankin da ta kasance a duniya da kuma matsayinta a kan Gaza ya sa ta zama babbar mai kare muradun Falasɗinu a cikin NATO.

Jami'an Amurka sun ce za su tattauna yakin Gaza da takwarorinsu na Turkiyya yayin taron na kwanaki uku.

"Idan ana batun Gabas ta Tsakiya, duba, na tabbata za a yi tattaunawa iri-iri, ciki har da tarukan da bangarorin biyu suka yi a gefen taron, inda za a yi maganar. amma a fili hakan yana da nasaba da tsaron yankin Tekun Atlantika na Turai, don haka abin da ke faruwa a yankin Gabas ta Tsakiya yana da matukar damuwa ga dukkanin shugabannin kungiyar ta NATO," in ji mai ba Biden shawara na musamman Mike Carpenter, gabanin taron.

A game da rawar da Turkiyya ta taka, ya ce: "Turkiyya na zaune a wani muhimmin waje, duka dangane da Gabashin Bahar Rum, da Kudancin Caucasus, da kuma Bahar Aswad."

"Abin da Turkiyya ta yi da yarjejeniyar Montreux na da matukar muhimmanci ta fuskar takaita jiragen yakin Rasha a cikin Tekun Bahar Aswad. Abokiya ce muhimmiya, kuma muna bukatar mu ci gaba da tattaunawa da ƙawayenmu na Turkiyya kan wannan batu."

Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka ta kuma amince da damuwar da Turkiyya ke da ita game da Gaza, inda mai magana da yawunta Mathew Miller ya tabbatar da tattaunawar da ake yi.

"Shugabannin Amurka za su ci gaba da tattaunawa da takwarorinsu na Turkiyya kan shirin tsagaita wuta a Zirin Gaza a yayin taron kungiyar tsaro ta NATO," kamar yadda Miller ya shaida wa TRT World, inda ya bayyana irin huldar diflomasiyyar da ake yi kan wannan batu.

Farfesa Bulent Gokay, Shugaban Makarantar Siyasa da Harkokin Kasa da Kasa da Muhalli (SPIRE) a Jami'ar Keele, ya yi bayani mai zurfi game da rikice-rikice biyu da ke fuskantar NATO.

Yakin da ake yi a Ukraine ya kasance babban kalubale ga wanzuwar kungiyar ta NATO, kamar yadda ya shaida wa TRT World.

"Ana sa ran taron zai tsawaita wata gada zuwa kungiyar NATO a Ukraine, amma ba tare da wani jadawali ba. A lokaci guda kuma, mai yiwuwa Turkiyya ta bukaci mambobin NATO da su yi duk abin da zai hana Isra'ila ci gaba da yaƙin Gaza. Sai dai kuma zai yi wahala kai tsaye shigar NATO a rikicin Gaza ba zai yiwu ba."

TRT World