Erdogan ya ce Ankara da Washington na da "dangantaka daban-daban" a fannonin tsaro da kasuwanci, yana mai cewa karfin kasuwancinsu ya haura dala biliyan 32. / Hoto: AA

Turkiyya ta gamsu ta kyautata hadin gwiwa da Amurka a cewar Shugaban kasar, Recep Tayyip Erdogan.

"Mun warware duk wasu matsaloli da ke tsakanin kasashenmu biyu a tattaunawar da muka yi da Shugaba Joe Biden, kuma a karshe mun yanke shawarar ci-gaba da tattaunawa a wasu hanyoyin," in ji Erdogan a ranar Litinin yayin wani zaman karawa juna sani da ya yi a birnin New York, inda yake halartar Babban Taron Majalisar Dinkin Duniya UNGA.

Shugaban Turkiyya ya ce "kasashenmu biyu za su karfafa hadin gwiwar da ke tsakaninmu wajen yaki da ta'addanci", da a cewarsa "hakan na barazana ga kasashen biyu."

Kan batun tallafin da Amurka ke bai wa 'yan ta'adda na kungiyar YPG/PKK a arewacin Siriya kuwa, Erdogan ya jaddada cewa ba za a hada kai da ko wacce kungiyar ta'addanci ba.

“Duk wani cigaba da aka samu a yankinmu na nuni kan rashin karfafa ayyukan ‘yan ta’adda na kwarai da wadanda ba na kwarai ba, don haka babu wata tattaunawa ta sulhu da ‘yan ta’adda, sannan ba za a kulla wata alaka ta abota ko kawance da su ba," a cewar Erdogan.

A jawabinsa, Erdogan ya bayyana gudunmawar Turkiyya wajen magance matsalolin da suka shafi duniya da kuma kokarinta wajen samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali da magance rashin adalci a tsare-taren kasa da kasa.

A bangaren yakin da ake yi a Ukraine kuwa, Erdogan ya ce Ankara na aiki tukuru don kawo karshen rikicin da kuma samar da zaman lafiya mai dorewa. Ya jaddada kudirin kasar na amfani da diflomasiyya a matsayin hanyar samar da zaman lafiya na dindindin a dukkan yankunan da ke fama da rikici da kuma fadada hanyoyin sada zumunta na duniya.

Shugaban ya kuma bayyana muhimmancin karfafa hadin kan kasa da kasa, musamman a yaki da kungiyoyin ta'addanci irinsu PKK da Daesh da kuma kungiyar ta'addanci ta Fetullah FETO, wacce a shekarar 2016 ta kaddamar da juyin mulkin da bai yi nasara ba a Turkiyya al'amarin ya yi sanadiyar kashe daruruwan mutane.

Ya kuma jaddada bukatar mayar da 'yan gudun hijirar Siriya cikin mutunci da kariya zuwa kasarsu ta asali.

Inganta hanyoyi : 'dama ta gina sabuwar duniya'

Turkiyya za ta samu dama ta gina sabuwar duniya a matakan da aka dauka a aikin inganta hanyar kasar Iraki, da zai hada kudancin kasar da makwabciyarta Turkiyyya, a cewar Shugaban na Turkiyya a ranar Litinin.

"Mun ga yadda kasashen yankin Gulf suka yi azama. Mu ma mun kuduri aniyar yin hakan," in ji shi, yana mai cewa su ma Amurka da Jamus da kuma Japan sun bayyana bukatarsu.

Da yake amsa tambaya game da rawar da Turkiyya ke takawa a matsayinta na mamba a kungiyar tsaro ta NATO da muradunta na kasa da kuma tashe-tashen hankulan siyasa da ake samu, Erdogan ya ce Turkiyya na daya daga cikin tsoffin mambobin kungiyar NATO kuma tana cikin kasashe biyar masu muhimmanci a cikin kungiyar kawancen.

Kazalika ya bayyana kokarin da yake yi wajen farfado da yarjejeniyar hatsi da aka kulla na tekun Bahar Aswad, Erdogan ya ce a ganawar da ya yi Shugaba Putin na Rasha a farkon watan nan, sun tattauna batun jigilar ton miliyan daya na hatsi zuwa kasashen Afirka.

Karanta labari mai alaka: Matsayin Turkiyya na taimaka wa Ukraine 'bai sauya ba': Fidan

Erdogan ya ce ya ba da shawarar a kara yawan hatsin, ya shaida wa Putin cewa ton miliyan daya "ya yi kadan." "A karshe dai mun amince kan karasa tattaunar "diflomasiyya ta hanyar ytarho," in ji shi.

Kan batun matsalar kwararar 'yan gudun hijira a duniya kuwa, Erdogan ya ce a halin da ake ciki Turkiyya na tsugunai da ‘yan gudun hijira kusan miliyan biyar, kuma za ta ci gaba da karbar bakuncinsu.

Sai dai Turkiyya na karfafa batun mayar da 'yan gudun hijirar Siriya wadanda ke son komawa kasasrsu ta asali cikin aminci, a cewar Erdogan, kasarmu tana kokarin gina gidaje a arewacin Siriya tare da tallafin kasar Qatar.

Idan aka kammala gina matsugunan na dindindin, ‘yan Siriya miliyan daya za su iya komawa kasarsu, kuma ya zuwa yanzu kusan dubu 600 sun fara komawa, in ji shi.

A halin yanzu dai shugaba Erdogan yana birnin New York don halartar taro babban taron Majalisar Dinkin Duniya karo na 78.

Ana sa ran nan ba da jimawa ba zai gabatar da jawabinsa a zauren taron.

TRT World