Firaministan Norway Jonas Gahr ya ce "ba za a samu zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba in har ba a amince da ƙasar Falasɗinu ba." Hoto: AA Archive

Turkiyya ta yi farin ciki da sanarwar da Sifaniya da Ireland da Norway suka fitar cewa sun amince da Falaɗinu a matsayin ƙasa, a cewar sanarwar ma'aikatar harkokin wajen ƙasar.

"Amince da Falasɗinu wani tanadi ne na dokokin duniya, da adalci da sanin ya kamata," kamar yadda Ma'aikatar Harkokin Wajen Turkiyya ta fitar a shafin X ranar Laraba.

Sanarwar ta jaddada cewa wannan wani muhimmin mataki ne wajen mai do da haƙƙin Falasaɗinawa da ke ƙarƙashin mamaya, da mayar da Falasɗinu wajen da ya dace da ita a harkokin ƙasashen duniya.

Ma'aikatar ta bayyana cewa Turkiyya ta ƙuduri aniyar ci gaba da ƙoƙarinta wajen ganin ƙarin ƙasashe sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa.

Ƙara mayar da Isra'ila saniyar ware

Norway da Ireland da Sifaniya sun bayyana a ranar Laraba cewa sun amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa, a wani mataki na tarihi da ya sha Allah-wadai daga Isra'ila da kuma murna daga Falasɗinawa.

Amincewar da ƙasashen uku suka yi a hukumance da kasancewar ƙasar Falasɗinawa 'yantacciya wanda zai fara aiki daga ranar 28 ga watan Mayu, a cewar shugabannin ƙasashen.

Nan take Isra'ila ta umarci jakadunta daga Norway da Ireland su koma gida.

Firaministan Norway Jonas Gahr Store ya ce "ba za a taɓa samun zaman lafiya a Gabas ta Tsakiya ba in ba a amince da Falasɗinu a matsayin ƙasa ba."

A cikin makonnin da suka gabata ƙasashen Tarayyar Turai da dama sun nuna shirinsu na amince wa da Falasɗinu a matsayin ƙasa, suna masu cewa samar da ƙasashe biyu abu ne mai muhimmanci don samar da zaman lafiya mai ɗorewa a yankin.

Matakin zai iya samun tagomashi wajen amince wa da ƙasar Falasɗinu daga sauran ƙasashen Turai, sannan zai ƙarfafa matakin a Majalisar Ɗinkin Duniya da ƙara mayar da Isra'ila saniyar ware.

TRT World