Ya kamata Netanyahu, 'mai kashe mutanen Gaza,' ya fuskanci shari'a kan aikata laifukan yaki: Erdogan

Ya kamata Netanyahu, 'mai kashe mutanen Gaza,' ya fuskanci shari'a kan aikata laifukan yaki: Erdogan

A shirye Turkiyya take ta zama kasa mai tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasdinu, in ji Shugaba Erdogan na Turkiyya.
A shirye Turkiyya take ta zama ƙasar da za ta shiga tsakani don samar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinu,in ji Recep Tayyip Erdogan said. / Photo: AA

Shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ya kamata Firaministan Isra'ila Benyamin Netanyahu ya fuskanci shari'a kan zamowarsa "mai aikata laifukan yaƙi," in ji shugaban kasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, yana mai kiransa da "mai kashe mutanen Gaza."

"Ba za mu bari a manta da batun mallakar makamin nukiliyar Isra'ila ba," in ji Erdogan da yake jawabi a wajen bude taron Ƙungiyar Hadin kan Ƙasashen Musulmai ta OIC a Istanbul a ranar Litinin.

Waɗanda ke yin biris da kashe-kashen da ake yi a Gaza ta hanyar ƙin cewa komai, har ma suke halasta hakan a karkashin kungiyar Hamas, ba su da wata magana da za su yi da sunan nuna tausayin bil'adama, in ji Erdogani a taron ministoci na 39 na Kwamitin Tattalin Arziki da Kasuwanci na OIC.

"Isra'ila ba ga kisan kai kawai ta tsaya ba, har ma sata tana yi," a cewar Erdogan, yana mai ƙarawa da "Ba za mu sake barin Isra'ila ta sake mamayar Gaza ba."

"Akwai wani tsari na duniya da ke kare muradun ƙasashe ƙalilan. Akwai buƙatar sauya tsatrin MDD da ke baibaye da maguɗi."

Shugaban na Turkiyya ya ce ƙin jinin Musulunci yana watsuwa kamar wata annoba a Ƙasashen Yamma.

A shirye Turkiyya take ta zama ƙasar da za ta shiga tsakani don samar da tattaunawar zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, ya ƙara da cewa.

"Gaza yankin Falasɗinu ne, Gaza mallakin Falasɗinawa ce kuma za ta ci gaba d akasancewa haka har abadam" in ji shugaban ƙasar Turkiyyan.

"Waɗanda suka kutsa Gaza za su nemi kutsawa wasu wuraren a gobe. Mai kisan mutanen Gaza Netanyahu ya bayyana cewa yana da muradun faɗaɗa mamayarsa," Erdogan ya faɗa.

Dabbancin Isra'ila

Da yake sukar matakin da Majalisar Dinkin Duniya ta dauka kan hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza, Erdogan ya ce, mambobin kwamitin sulhun sun yi zagon ƙasa ga kokarin babban sakataren MDD Antonio Guterres.

Fiye da jami'an MDD 100 ne aka kashe a hare-harem Isra'ila a Gaza, kamar yadda Erdogan ya fada, yana mai ƙarawa da cewa, MDD, wacce aka kafa ta don samar da tsari da zaman lafiya a duniya, ta gaza ko da kare ma'aikatanta daga "dabbancin Isra'ila."

Da yake tunawa da kudurin MDD da ya buƙaci a samar da tsagaita wuta, mai ɗorewa tsakanin Isra'ila da Hamas a Gaza a ranar 27 ga Oktoba, Erdogan ya ce wannan mataki ne mai ƙima na wakiltar lamirin bil'adama.

"Kazalika, saboda tsarin da ake da shi na Majalisar Ɗinkin Duniya, wannan shawarar ta zama marar amfani."

Ya ce an yi watsi da ra'ayin ƙasashen da suka kaɗa ƙuri'ar amincewa da ƙudurin da kuma waɗanda suka ƙaurace.

"Wannan hujja kadai ta isa ta nuna yadda ake killace duniyar Musulmai mai yawan jama'a biliyan biyu. Akwai tsarin duniya wanda ke aiki da nufin wasu ƙasashe. Akwai buƙatar a sauya tsarin cin hanci da rashawa na Majalisar Dinkin Duniya."

Da sanyin safiyar Juma'a ne sojojin Isra'ila suka sake kai hare-hare a Zirin Gaza bayan ayyana kawo ƙarshen dakatar da ayyukan jinƙai na tsawon mako guda.

Isra'ila ta ƙaddamar da hare-hare ba ƙaƙƙautawa ta sama da ta ƙasa a Gaza tun bayan harin ba-zata da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa ta Hamas ta kai Isra'ila ranar 7 ga watan Oktoba.

Adadin waɗanda suka mutu a hare-haren da Isra'ila ke kaiwa Gaza ya kai 15,523 tun farkon rikicin a ranar 7 ga watan Oktoba, in ji ma'aikatar lafiya a yankin Falasdinawa da aka yi wa ƙawanya a ranar Lahadi.

TRT World