Yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinawa na ci gaba da kazanta sakamakon yadda adadin wadanda ake kashewa yake karuwa. Hoto/Getty Images

Dakarun Isra'ila sun kai sabbin hare-hare ta sama a yankin Falasdinawa da suka mamaye bayan kungiyar Hamas ta shammace su ta kutsa kai cikin Isra'ila ranar Asabar. Kawo yanzu an kashe fiye da mutum 500 daga bangarorin biyu.

15:30 GMT — Shugaban Turkiyya Erdogan ya yi kira kan a tsagaita wuta

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya bukaci Isra’ila da Hamas su tsagaita wuta, inda ya ce bai kamata a jinkirta samun ‘yancin kan Falasdinu ba a matsayin kasa mai cin gashin kanta mai hedikwata a Birnin Kudus, kamar yadda aka amince a yarjejeniyar 1967.

Shugaba Erdogan ya bayyana haka ne a lokacin da yake jawabi a wani taro wanda aka gudanar a Cocin Mor Efrem Syriac a birnin Santambul.

Shugaba Erdogan ya ce a shirye Turkiyya take ta bayar da gudunmawa domin ganin Isra’ila da Falasdinawa sun tsagaita wuta.

1423 GMT — An kashe sama da Yahudawa 600 a Isra'ila

Adadin mutanen da suka mutu a Isra'ila sakamakon yakin da ake gwabzawa tsakanin Falasdinawa da Isra’ila ya kai 600, kamar yadda kafafen watsa labarai da ke yankin da rikicin ke faruwa suka ruwaito.

Sama da mutum 2,000 aka raunata zuwa yanzu, kamar yadda tashar talabijin ta Hebrew 13 ta ruwaito.

Hukumar Tsaron Isra’ila a ranar Lahadi ya wallafa sunayen sojoji 26 wadanda aka kashe a lokacin da aka yi arangama tsakanin mayakan Hamas da Yahudawa a kan iyakar Gaza a ranar Asabar.

Haka kuma akwai Yahudawa sama da 100 wadanda aka yi garkuwa da su zuwa Gaza a ranar Asabar.

1200GMT — Nijeriya ta yi kira ga Falasdinawa da Isra’ila su tsagaita wuta

Gwamnatin Nijeriya ta nuna matukar damuwa kan yadda aka soma rikici tsakanin Isra’ila da kuma kungiyar Hamas ta Falasdinawa a ranar Asabar.

A wata sanarwa da gwamnatin kasar ta fitar ta ofishin Ministan Harkokin Wajen Nijeriya Ambasada Yusuf M. Tuggar, kasar ta nemi duka bangarorin biyu su tsagaita wuta.

“Don haka Gwamnatin Tarayyar Nijeriya na kira ga bangarorin biyu da su dakata, tare da bayar da fifiko kan tsaron lafiyar fararen hula da ba da damar kula da ayyukan jin kai,” in ji sanarwar.

Haka kuma gwamnatin Nijeriyar ta yi kira da a yi kokarin sasantawa ta hanyar hawa kan teburin sulhu.

1130 GMT — Dan sanda a Masar ya kashe Yahudawa biyu a wurin yawon bude ido

Rahotanni sun ce tuni aka kama dan sandan. Hoto/Reuters

Wani dan sanda a birnin Masar ya bude wuta kan wasu Yahudawa masu yawon bude ido a birnin Alexandria da ke gefen Bahar Rum, inda ya kashe akalla Yahudawa biyu da wani dan Masar daya, kamar yadda kafafen watsa labarai suka ruwaito.

Wata kafar watsa labarai ta Extra News wadda ke da alaka da hukumomin tsaron Masar sun ruwaito wani jami’in tsaro wanda ba a bayyana sunanshi ba inda yake cewa an raunata wani a harin da aka kai a ranar Lahadi a wani wurin yawon bude ido na the Pompey’s Pillar da ke Alexandria.

Rahotanni sun ce an kama dan sandan da ya yi kisan. Masar ta sasanta da Isra’ila tsawon shekaru inda kuma ta kasance mai shiga tsakani a rikicin da ake yawan yi tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Sai dai ana yawan nuna kiyayyar Yahudawa a kasar musamman a lokutan da ake samun rikici tsakanin Falasdinawa da Isra’ila.

1042GMT — Jami'in Isra'ila ya ce akwai yiwuwar shafe makonni ana fafatawa

Wani babban jami’in Isra’ila a ranar Lahadi ya tabbatar da an samu “babbar gazawa a leken asiri” a makonnin da suka gabata wanda a cewarsa ya jawo babban rikici tsakanin Isra’ila da Falasdinawa.

Jami’in wanda ya bukaci a sakaya sunansa ya bayyana cewa ana sa ran za a tsawaita wannan yakin zuwa “makonni” kamar yadda ya shaida wa tashar talabijin ta Hebrew 13.

Hamas ta kaddamar da wani samame mai suna Operation Al-Aqsa Flood a ranar Asabar inda kuma kungiyar ta ce sun kai wannan samamen ne domin mayar da martani kan yadda ake kai musu samame a Masallacin Birnin-Kudus da kuma karuwar Yahudawa da ke mamayesu.

Zuwa yanzu dai akalla Falasdinawa 313 aka kashe sa’annan kusan 2,000 suka samu raunuka a hare-haren da aka kai, kamar yadda likitoci a birnin Gaza suka tabbatar, inda wadanda aka kashe a Isra’ila suka tasar wa 350.

0745 GMT — Isra'ila ta kashe Falasdinawa 313 ya zuwa wannan lokaci

Hare-haren da Isra'ila ta kai wa Falasdinawa a Zirin Gaza don martani kan kutsen da Hamas ta yi mata ranar Asabar sun yi sanadin mutuwar akalla Falasdinawa 313, a cewar Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Falasdinu.

A sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ta kara da cewa an jikkata Falasdinawa 1,990 a yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza.

A nata bangaren, Isra'ila ta ce an jikkata 'yan kasarta 1,864 a fafatawar da ake yi tsakanin su da Falasdinawa a Gaza kawo yanzu, ciki har da mutum 345 da ke mawuyacin hali, in ji wata sanarwar Ma'aikatar Lafiya ta Isra'ila.

An kashe akalla 'yan Israi'la 350, in ji gidan talbijin na Channel 12.

Sanarwar ta kara da cewa an jikkata Falasdinawa 1,990 a yayin da Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta a Gaza./Hoto: Reuters 

0630 GMT — An kashe Falasdinawa akalla 256 a hare-haren Isra'ila kawo yanzu

Ma'aikatar Kiwon Lafiya ta Gaza ta ce kawo yanzu hare-haren da Isra'ila take kai wa a Zirin Gaza don mayar da martani kan harin da Hamas ta kai mata sun yi sanadin mutuwar Falasdinawa akalla 256, ciki har da kananan yara 20.

Sanarwar da ma'aikatar ta fitar ranar Lahadi ta kara da cewa an jikkata Falasdinawa 1,788, da suka hada da kananan yara 121,

A bangare daya, an jikkata 'yan Isra'ila 1,864 a fafatawar da ake yi tsakanin su da Falasdinawa a Gaza kawo yanzu, ciki har da mutum 345 da ke mawuyacin hali, in ji wata sanarwar Ma'aikatar Lafiya ta Isra'ila.

Kazalika a wata sanarwar ta daban, rundunar sojin Isra'ila ta ce “dakarumu suna ci gaba da kai hare-hare a fadin Zirin Gaza” ciki har da gine-ginen gwamnati.

“Jiragen yaki sun kai hari a wani ginin sojoji da ke gidan shugaban hukumar leken asiri ta 'yan ta'adda na Hamas,” in ji rundunar sojin.

0600 GMT — Sojojin Isra'ila akalla 750 sun bata

Sojojin Isra'ila akalla 750 sun bata tun bayan da rikici ya barke tsakanin dakarun kasar da kungiyar Hamas ranar Asabar da safe, a cewar jaridar Jerusalem Post.

A wani sako da ta wallafa a shafin X, jaridar ta ce “rahotanni da ba na hukuma ba, sun bayyana cewa akalla sojojin Isra'ila 750 ne suka bata kawo yanzu.”

Hamas ta kaddamar da hari mai suna Operation Al-Aqsa Flood ranar Asabar a Isra'ila inda ta kashe daruruwan 'yan kasar sannan ta yi garkuwa da wasu daruruwa, tana mai cewa ta yi haka ne don martani ga Isra'ila kan mamayar Masallacin Kudus da kuma hare-haren da 'yan kama-wuri-zauna suke yawan kai musu.

Sai dai dakarun tsaron Isra'ila sun yi raddi da hare-hare ta sama a yankin Gaza inda suka kashe daruruwan mutane.

Har yanzu ana ci gaba da fafatawa tsakanin dakarun Isra'ila da mayakan Hamas./Hoto:AA

0523 GMT — Hezbollah ta dauki alhakin kai wa Isra'ila hari

Kungiyar Hezbollah ta kasar Lebanon ta dauki alhakin kai hare-haren rokoki da igwa a yankin Shebaa Farms na Isra'ila, tana mai cewa ta yi hakan ne domin "nuna goyon baya" ga al'ummar Falasdinu.

A wata sanarwa da ta fitar, kungiyar ta ce ta kai hare-haren ne a yankuna uku ciki har da "radar site" da ke Shebaa Farms, wato wani yanki da Isra'ila ta mamaye tun 1967 wanda Lebanon ta yi ikirarin cewa mallakinta ne.

Isra'ila ta mayar da martani ta hanyar kai harin giwa a kudancin Lebanon.

0500 GMT — Tarayyar Afirka ta yi kira a tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da Falasdinawa

Kungiyar Tarayyar Afirka ta bayyana "matukar damuwa" game da rikicin da ya barke tsakanin Isra'ila da Falasdinawa tana mai cewa zai yi "mummunan tasiri" kan fararen-hula da kuma zaman lafiyar yankin.

''Hana Falasdinawa 'yanci, musamman hana su zama kasa mai 'yancin kanta, shi ne musabbabin rashin jutuwa tsakanin Isra'ila da Falasdinawa,'' a cewar shugaban Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat a wata sanarwa da ya fitar.

Moussa Faki Mahamat ya yi kira ga kasashen duniya su sa baki don ganin an samu kasar Falasdinawa da ta Isra'ila./Hoto: Kungiyar Tarayyar Afirka

Shugaban Tarayyar Afirka ya yi kira ga bangarorin da ke rikici su yi gaggawar "kawo karshen hare-haren soji sannan su koma kan teburin sulhu, ba tare da wasu sharuda ba, don tabbatar da an samu kasashe biyu masu zaman kansu.''

0430 GMT — China na "matukar nuna damuwa" kan rikicin Isra'ila da Falasdinawa

China ta ce ta "damu matuka" a kan yadda rikici tsakanin Isra'ila da Falasdinawa ya rincabe da sauri a karshen mako, inda ta yi kira da dukkan bangarorin su "mayar da wukar".

"China ta damu matuka game da halin da ake ciki a yanzu na rincabewar rikici tsakanin Falasdinawa da Isra'ila," a cewar Ma'aikatar Tsaron Kasar da ke Beijing, sannan ta kara da "kira ga dukkan bangarorin da lamarin ya shafa su mayar da wukar kube, su tsagaita wuta nan-take, kana a kare fararen-hula da kuma takaita yaduwar rikicin".

0400 a agogon GMT —Isra'ila za ta katse lantarki sannan ta daina kai abinci Zirin Gaza

Isra'ila za ta katse wutar lantarki, sannan ta hana shigar da kayan abinci yankin Gaza da ta dade da mamayewa, in ji wata sanarwa da ta fito daga ofishin Firaiminista Benjamin Netanyahu a yayin da take ci gaba da matsa kaimi wurin kai hare-hare kan yankunan Falasdinawa.

Isra'ila ta umarci Falasdinawa su fice daga Gaza./Hoto:AA

Kazalika Netanyahu ya ce majalisar tsaron kasarsa ta amince a rusa gine-ginen soji da na gwamnatin kungiyoyin Hamas da Islamic Jihad da ke yankin Gaza da ta mamaye.

03:50 a agogon GMT — Jiragen yakin Isra'ila sun kai hari a Masallaci

Jiragen yakin Isra'ila ranar Asabar sun kai hari a masallatai da ke yankin Gaza da aka mamaye.

Jiragen sun kai farmaki a masallacin Habib Muhammad da ke unguwar El-Yabani mai makwabtaka da birnin Khan Yunus a kudancin Zirin Gaza, a cewar wasu majiyoyi.

Rahotanni sun ce an rusa masallacin, kuma an nuna rika watsa yadda ake rusa shi a shafukan sada zumuna.

Kawo yanzu hukumomin Falasdinawa ba su fitar da sanarwa game da rusa masallacin ba.

Kamfanin dillancin labaran Anadolu na Turkiyya ya ambato wata sanarwar sojin Isra'ila tana cewa dakarun kasar sun kai hari a wani gida a Beit Hanoun a arewacin Gaza.

Hamas ta kaddamar da hari mai suna Operation Al Aqsa Flood ranar Asabar kan Isra'ila inda ta ce ta dauki matakin na ban mamaki ne domin yin raddi kan dakarun Isra'ila da suka mamaye Masallacin Kudus da kuma 'yan kama-wuri-zauna.

Sai dai ita ma Isra'ila ta kaddamar da hari mai taken Operation Swords of Iron a kan Hamas a Zirin Gaza inda kawo yanzu ta kashe daruruwan Falasdinawa.

AA