JORDAN-EGYPT/ / Photo: AP

1541 GMT –– Ba za a iya kawar da Hamas ba — in ji Masar da Jordan

Manyan jami'an diflomasiyyar Jordan da Masar sun ce ba za a iya kawar da kungiyar gwagwarmayar Falasdinawa ta Hamas ba a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai wa Gaza hari.

"Hamas wata aƙida ce da ba za a iya kawar da ita ba," in ji Ministan Harkokin Wajen Jordan Ayman Safadi a wani taron tattalin arziki na duniya a Saudiyya.

Ya ce kungiyar Falasdinawa ba ta kunna wutar rikicin da ake yi a Gaza ba.

Ya kara da cewa, ba a ranar 7 ga watan Oktoba matsalar ta fara ba, amma sakamakon shekaru 70 ne na mamayar da Isra'ila ta yi, wanda ya ƙi amincewa da hakkin Falasdinawa.

“Kowa yana son zaman lafiya ne bisa tsarin samar da kasashe biyu,” in ji Safadi. "Dole ne Isra'ila ta ayyana kudurin ta na samar da zaman lafiya mai cike da adalci, amma a bayyane yake cewa Netanyahu ba ya son zaman lafiya."

Shi ma a nasa bangaren Ministan Harkokin Wajen Masar Sameh Shoukry ya ce shugabannin Hamas sun yi nuni da cewa a shirye suke su yi watsi da adawa da makami "idan har akwai aniya ta fuskar kafa kasar Falasdinu."

"Yakin da ake yi da makami da tsayin daka na mamaya halal ne, kuma muddin aka samu mamaya za a samu hujjar yin tirjiya a karkashin dokokin kasa da kasa," kamar yadda ya shaida wa kwamitin.

Babban jami'in diflomasiyyar ya yi kira da a kafa sharuddan da za su kai ga Hamas ta kasance abokiyar ƙawance a tsarin [siyasa] da kuma shiga kafa kasar Falasdinu. Ya kara da cewa "An ba wa Falasdinawa masu kada kuri'a alhakin tantance irin rawar da Hamas za ta iya takawa."

1337 GMT –– Gadar da rundunar sojin Amurka za ta gina a Gaza za ta lashe dala miliyan 320

Kimanin kudin da rundunar sojin Amurka za ta kashe na gina gada a mashigar Zirin Gaza domin kai agajin jinƙai ya kai dalar Amurka miliyan 320, kamar yadda wani jami'in tsaron Amurka da wata majiya mai tushe suka shaida wa kamfanin dillancin labarai na Reuters.

Wannan adadi, wanda ba a bayar da rahoto kansa a baya ba, ya kwatanta irin gagarumin aikin gine-gine da Ma'aikatar Tsaron Amurka ta ce ma'aikatan Amurka kusan 1,000, galibi daga Sojojin ƙasa da na ruwa ne za su yi shi.

A yanzu, adadin kuɗin ya ninka kusan sau biyu daga ƙiyasin farko a farkon wannan shekarar, a cewar wani wanda ya san lamarin.

"Ba tashi kawai adadin ya yi ba, ya ƙaru ne matuƙa," kamar yadda Sanata Roger Wicker, babban dan jam'iyyar Republican a kwamitin kula da ayyukan soja na majalisar dattijai, ya shaida wa Reuters, lokacin da aka tambaye shi game da farashin.

"Wannan lamari mai haɗari tare da fa'ida kaɗan a yanzu zai ci kuɗin masu biyan haraji na Amurka aƙalla dala miliyan 320 don gudanar da aikin gina gadar har tsawon kwanaki 90 kacal."

1405 GMT –– An yi wa Hamas tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 a Gaza, da sakin fursunoni — Burtaniya

An yi wa kungiyar Hamas tayin tsagaita wuta na kwanaki 40 da kuma sakin “mai yiwuwa dubban” fursunonin Falasdinawan a matsayin mayar da martani ga ‘yantar da Isra’ilawa da aka yi garkuwa da su, in ji Sakataren Harkokin Wajen Birtaniya David Cameron.

An yi wa ƙungiyar gwagwarmayar Falasdinawa "tayin mai karimci na tsagaita wuta na tsawon kwanaki 40, da sako dubban fursunonin Falasdinawan, domin a sako wadannan mutanen da aka yi garkuwa da su", kamar yadda Cameron ya fada a taron dandalin tattalin arzikin duniya a Riyadh.

Ministan Harkokin Wajen Birtaniya ya ce, "idan har ana son mafitar siyasa ta samar da ƙasashe biyu", da bai wa ƙasar Falasdinu cin gashin kanta da zama lafiya da Isra'ila, "dole ne ƙungiyar da ke da alhakin harin 7 ga Oktoban 2023, wato Hamas ta bar Gaza tare da wargaza ayyukan ta'addanci a Gaza."

1407 GMT –– Isra'ila ta kaddamar da sabbin hare-hare a kudancin Lebanon

Isra'ila ta kai sabbin hare-hare a kudancin Lebanon a daidai da ake ƙara samun rashin jituwa tsakanin ƙungiyar Hezbollah ta Lebanon da ƙasar.

Isra'ila ta kai harin makaman atilari a garuruwan Ayta ash-Shaab da Alma ash-Shaab da Naqoura, kamar yadda kamfanin dillancin labarai na ƙasar Lebanon ya ruwaito.

Haka kuma rahotanni sun ce Isra'ilar ta kai hare-hare ta sama a kan garuruwan Tyre Harfa da Maroun al-Ras da Naqoura da Blat.

Babu wani ƙarin bayani dangane da waɗanda suka samu rauni sakamakon harin.

TRT Afrika da abokan hulda