Alƙalai 15 ne daga faɗin duniya suka yanke hukuncin, inda 13 suka amince da shi yayin da 2 suka yi fatali da shi - wato alƙali daga Uganda da kuma ita kanta Isra'ila.

Kotun Majalisar Ɗinkin Duniya ta umarci Isra'ila ta daina kai hare-hare a yankin Rafah da ke kudancin Gaza, a wani hukunci mai ƙarfafa gwiwa da ta yanke ranar Juma'a.

Alƙalin da ya jagoranci sauran alƙalai wurin yanke hukuncin, Nawaf Salam ya ce halin da ake ciki a Gaza ya taɓarɓare tun bayan umarnin da kotun ta bai wa Isra'ila na inganta lamura a yankin na Falasɗinu.

"Muna buƙatar ƙasar Isra'ila ta yi gagawar daina kai harin soji, da ma ɗaukar duk wani mataki a yankin Rafah, wanda ka iya jefa rayuwar Falasɗinawan da ke Gaza cikin bala'i," in ji shi.

Ya ƙara da cewa "dole ne Isra'ila ta buɗe iyakar Rafah ba tare da shamaki ba don a shigar da kayan buƙatun gaggawa da na agaji."

Alƙalai 15 ne daga faɗin duniya suka yanke hukuncin, inda 13 suka amince da shi yayin da 2 suka yi fatali da shi - wato alƙali daga Uganda da kuma ita kanta Isra'ila.

Alƙalan sun yanke hukuncin ne mako guda bayan buƙatar da Afirka ta Kudu ta shigar a gabanta ta neman ta ba da umarnin dakatar da farmakin da sojojin Isra’ila ke kai wa a Gaza, inda Pretoria ta zargi Isra’ila da ''kisan kiyashi.''

A wani hukunci da ta yanke a watan Janairu, kotun ta umarci Isra'ila da ta yi dukkan mai yiwuwa wajen hana aikata laifin kisan kiyashi a Gaza sai dai ba ta bayar da umarni kan tsagaita wuta ba.

Afirka ta Kudu ta ce harin da Isra'ila ta kai a Rafah na baya-bayan nan ya tsananta halin da ake ciki kuma ya kamata hakan ya tilasta wa kotun ta ba da sabbin umarnin gaggawa.

A wani zaman taron jin ra'ayin jama'a na kotun ICJ a makon da ya gabata, jakadan Afirka ta Kudu Vusimuzi Madonsela ya yi zargin cewa "kisan kiyashi da Isra'ila ke aikatawa ya tsananta kuma a yanzu ya kai wani sabon mataki mai ban tsoro".

''Duk da cewa buƙatar da ta taso a yanzu ta samo asali ne daga yanayin da ake ciki a Rafah, kana hare-haren da Isra'ila take yi a faɗin Gaza sun ƙara tsananta a cikin 'yan kwanakin da suka gabata, lamarin da ke buƙatar kulawar wannan kotu,'' in ji shi.

Afirka ta Kudu ta ce hanya ɗaya tilo da za a iya kai kayayyakin jinƙai don taƙaita raɗaɗin rikicin Gaza tana rufe sakamakon mamayar sojin Isra’ila.

TRT Afrika da abokan hulda