Aikin Hajji wajibi ne ga Musulman da suke da hali aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu. / Photo: AFP

Dubban Falasɗinawa ba za su samu damar zuwa aikin Hajjin bana ba saboda Isra'ila ta mamaye yankin Rafah da ake wucewa domin fita daga yankin Gaza, a cewar Ma'aikatar Harkokin Addini da Awqaf ta Falasɗinu.

"Hana dubban al'ummar Gaza tafiya aikin Hajji keta 'yancin mutane ne na gudanar da addininsu da ma dokokin ƙasashen duniya," in ji wata sanarwa da ma'aikatar ta fitar ranar Laraba.

"Wannan sabon laifin yaƙi ne cikin jerin laifukan yaƙin da masu mamaya na Isra'ila suke yi wa al'ummarmu da wuraren gudanar da ibadarmu," a cewar sanarwar.

Ranar 7 ga watan Mayu sojojin Isra'ila suka mamaye yankin Rafah na Falasɗinu da ke kan iyaka da Masar, kuma nan ne kaɗai hanyar da ake bi wurin fita daga Gaza don zuwa wasu sassan duniya.

Aikin Hajji yana cikin shika-shikan Musulunci kuma wajibi ne ga Musulman da suke da hali aƙalla sau ɗaya a rayuwarsu.

Ƙaddamar da hare-hare ta ƙasa a yankin Rafah

Ma'aikatar Harkokin Addini da Awqaf ta Falasɗinu ta yi kira ga Masar da Saudiyya su matsa lamba kan Isra'ila domin “bai wa al'ummar Gaza damar gudanar da aikin Hajjin bana.”

Ranar 6 ga watan Mayu dakarun Isra'ila suka ƙaddamar da hare-hare a Rafaha da ke kudancin Gaza, inda Falasɗinawa fiye da miliyan 1.5 suke samun mafaka bayan mahukuntan birnin Tel Aviv sun ƙaddamar da hare-hare a yankin.

Hukumar Majalisar Ɗinkin Duniya mai kula da Falasɗinawa 'yan gudun hijira (UNRWA) ta ƙiyasta cewa fiye da mutum 800,000 sun tsere daga birnin tun da Isra'ila ta kaddamar da hare-hare a watan Oktoban da ya gabata.

Isra'ila ta lalata galibin gine-ginen da ke Gaza, sannan ta hana shigar da kayan abinci da magunguna da samar da ruwa mai tsafta a watannu bakwai da ta shafe tana kai hare-hare a yankin.

TRT World