Turkiyya na kan gaba wurin shigar da kayan agaji yankin Gaza, wadanda suka haɗa da abinci da magunguna, tare da kwashe dubban marasa lafiya domin kula da su. /Hoto: AA

Turkiyya ta dakatar da fitar da dukkan kayayyaki da kuma shigar da su Isra'ila, a matsayin wata hanya ta ƙuntata wa mahukuntan Tel Aviv saboda yaƙin da suke yi a Gaza wanda ya kashe Falasɗinawa fiye da 34,596 a cikin wata shida.

"Turkiyya za ta aiwatar da waɗannan sabbin matakai har sai gwamnatin Isra'ila ta bari a shiga da kayan agaji Gaza ba tare da katsalandan ba," a cewar ma'aikatar cinikayya ta Turkiyya.

Sanarwar ta ƙara da cewa, "An aiwatar da mataki na biyu na wannan shiri, kuma an dakatar da fitar da kayayyaki zuwa Isra'ila da kuma shigo da su daga can".

A watan jiya ne hukumomi a Ankara suka sanya wa Isra'ila wasu tankunkuman kasuwanci, suna masu cewa ba za su ɗage su ba sai ta tsagaita wuta a yaƙin da take yi a Gaza tare da bari a shiga da kayayyakin agaji ba tare da shamaki ba.

An dakatar da fitar da nau'ukan kayayyaki 54

Kayayyakin da aka dakatar da fitarwa zuwa Isra'ila sun haɗa da nau'uka daban-daban na gorar-ruwa da baƙin-ƙarfe da fenti da wayoyin lantarki da kayayyakin gini da fetur da dangoginsa.

Turkiyya na sawun gaba wajen caccakar Isra'ila tun da ta ƙaddamar da hare-hare a Gaza ranar 7 ga watan Oktoba inda take aikata ɗaya daga cikin ɓarna mafi girma da aka yi a wannan zamani.

Kazalika ma'aikatar cinikayyar ta ce Turkiyya ta daɗe da “bari a sayar wa Isra'ila duk wani kaya da ake amfani da shi wajen harkar soji.”

“Jamhuriyar Turkiyya da al'ummarta za su ci gaba da goyon bayan Falasɗinu da al'ummarta, kamar yadda muka yi tun da farko."

Isra'ila ta rusa akasarin gine-ginen da ke Gaza, sannan ta tilasta wa mutum fiye da miliyan 1.9 yin gudun hijira, inda suke fama da cututtuka da bala'in yunwa.

TRT World