| Hausa
TURKIYYA
2 minti karatu
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Sabuwar dokar Turkiyyar, wadda za ta fara aiki ranar 1 ga watan Nuwamba, na buƙatar tantance shekaru ta shafin gwamnati mai ɗauke da bayanan 'yan ƙasa na e-Devlet tare da hana kafafan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekaru 15 hidima.
Turkiyya ta haramta wa shafukan sada zumunta yi wa 'yan ƙasa da shekara 15 rijista
Ba za a bai wa kamfanonin shafukan sada zumunta damar aiki da yara 'yan ƙasa da shekara 15 ba.

Shafin gwamnatin Turkiyya ya wallafa wata sabuwar doka ranar Asabar kan tabbatar da shekarun masu amfani da shafukan sada zumunta, inda ta hana shafukan sada zumunta bai wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 damar amfani da su.

A ƙarƙashin dokar, wadda ɓangaren tsaron intanet na fadar shugaban ƙasar ya tsara, za a tabbatar da shekaru ne ta hanyar shafin gwamnati mai ɗauke da bayanan ‘yan ƙasa wato e-Devlet.

Ba za a bai wa kamfanonin shafukan sada zumunta damar yi wa yara ‘yan ƙasa da shekaru 15 hidima ba. Shafukan yara da suka riga suka cika shekara 15 kuwa za a ba su wasu saƙonnin ne kawai da suka fi dacewa da matakin girmansu na zahiri da tunani da ƙwakwalwa da kuma zuciya.

Dokar na buƙatar shafukan su ayyana tsarin kare sirri mai tsauri ka shafukan yara, su ayyana su a matsayin na sirri da kuma hana su iya watsa bidiyo kai tsaye da kuma talla na musamman dominsu.

Kazalika dole shafukan sada zumuntan su tabbatar da cewa yara za su iya karɓar saƙonnin ne kawai daga shafukan da suke bi, kuma a ɓoye mabiyansu da waɗanda suke bi daga sauran masu amfani da shafukan.

An kuma buƙace su su ba da iko da iyaye za su iya amfani da su wajen taƙaita tsare-tsaren shafukan yaransu da kuma ikon amincewa da cinikayya a shafukan yaran.

Dokar za ta fara aiki ne ranar 1 ga watan Nuwamba. Dole a tantance shekaru na shafukan da ke aiki a yanzu zuwa ranar 31 ga watan Maris na shekarar 2027, kuma za a rufe shafukan da aka gane cewa na ‘yan ƙasa da shekaru 15 ne.

Rumbun Labarai
Turkiyya za ta ci gaba da magana kan Falasɗinawa: Erdogan
Zauren kotu ya dace da masu aikata laifukan yaƙi ba zauren Majalisar Ɗinkin Duniya ba: Erdogan
Jami’an Sojin Ruwa 30 na Saudiyya sun kammala karɓar horo a kamfanin tsaron Turkiyya, Baykar
Yadda Turkiyya ke taimaka wa Iraƙi wajen isar da albarkatun manta zuwa kasuwannin ƙasa da ƙasa
An wallafa jawabin Shugaba Erdogan na UNGA-81 a matsayin littafi cikin harsuna uku
Shugaban Turkiyya Erdogan ya buƙaci haɗin ƙan Musulmai, ya soki nuna wariya
Emine Erdogan ta buƙaci a rabu da ‘al’adar jefar da kaya' a koma ga tsarin sabuntawa
Erdogan ya yi kira da a gyara MƊD, ya nemi a soke ikon kujerar na-ƙi
Abincin Afirka daga Turkiyya
Shugaba Erdogan na Turkiyya ya tafi New York taron Majalisar Dinkin Duniya
'Turkiyya za ta duba buƙatun Saudiyya ƙarƙashin yarjejeniyar Makkah yayin da Houthi ke kai hari'
An gano kwanson wani dodon koɗi mai shekara 66,000 a Ankara babban birnin Turkiyya
Turkiyya ta yi zarra a Shirin Ƙimar Dalibai na Duniya (PISA) 2025 a tsakanin ƙasashen OECD
Turkiyya ta yi Allah wadai kan girmama Ratko Mladic da aka yanke wa hukuncin laifin yaƙi
Turkiyya ba za ta bari a toshe hanyar ci-gabanta ba: Erdogan
Jiragen ruwa biyu na kasuwanci sun yi karo a gabar Tekun Silivri a Istanbul, mutum 10 sun ɓata
30 ga Agusta: Nasarar da ta buɗe hanyar tasowar Turkiyya ta zamani
An haƙo wani sassaƙen ɗan'adam zaune a kan damisa mai shekaru 11,000 a Turkiyya
Turkiyya ta ƙara haɓaka kasuwancin da take yi da ƙasashen Musulmi
Aselsan: Kamfanin tsaro na Turkiyya zai baje-kolin jirgin ƙarƙashin ruwansa a bikin Teknofest