Kamfanin Siminti na Dangote ya karrama ƙwararrun direbobi 35 daga cikin masu tukin motocin da ke ƙarƙashin tsarin jigilar kayayyakin kwastomominsa a faɗin Najeriya, bisa jajircewarsu wajen kiyaye dokokin hanya da tukin ganganci.
Biyar daga cikin waɗanda suka samu kyaututtukan da suka fito daga shiyyar Arewa ta Tsakiya, sun karɓi lambobin yabo da kyaututtuka a wani bikin karramawa na shirin ƙarfafa masu motocin kwastomomi na shekarar 2026 (CTES), wanda aka gudanar a Abuja ranar Talata, 24 ga Nuwamba.
Taken bikin shi ne, “Lada Ga Nagartar Aiki Wajen Samar da Hanyoyi Masu Aminci.” An gudanar da bikin ne domin karrama direbobin da aka zaɓa daga cikin motocin da suka haura 2,500 da ke ƙarƙashin tsarin jigilar kayayyakin kwastomomin kamfanin a faɗin ƙasar.
Da yake jawabi a madadin rukunin kamfanin, Daraktan Talla na Ƙasa, Mista Dolapo Ali, ya ce faɗaɗa hanyoyin rarraba kayayyakin kamfanin ya ƙara muhimmancin inganta matakan kula da lafiyar masu amfani da tituna.
Ya bayyana cewa kamfanin Siminti na Dangote ya samu raguwar haɗurran ababen hawa a kan tituna da kashi 60 cikin 100, sakamakon ci gaba da zuba jari wajen horas da direbobi, sa ido kan harkokin tsaro da kuma karrama ma'aikatan da suka nuna ƙwarewa.
Ali ya ce wannan sabon cigaba ya biyo bayan raguwar haɗurra da kashi 30 cikin 100 da aka samu a shekarar 2023, bayan ƙaddamar da shirin inganta tsaron tuki na kamfanin.
A cewar sa, shirin ya ƙunshi horaswa ta musamman ga kusan direbobin manyan motoci 3,000 kan dabarun tuƙi cikin taka-tsan-tsan da kuma bin dokokin kiyaye lafiyar hanya.
Ya danganta nasarar da aka samu da shirye-shiryen horaswa akai-akai, sa ido sosai kan halayen direbobi yayin tuki, ɗaukar matakan gyara a kan lokaci da kuma bayar da ƙarfafa gwiwa domin inganta ɗabi'ar tukin da ya dace.
Ali ya kuma bayyana cewa tsarin jigilar kayayyakin kwastomomin kamfanin ya bunƙasa sosai, inda adadin motocinsa ya ƙaru daga 469 a shekarar 2017 zuwa sama da 2,500 a halin yanzu.
Ya ce wannan faɗaɗa aiki ya sa ya zama wajibi kamfanin ya ƙara ƙarfafa matakan tsaro tare da inganta yadda yake kula da direbobinsa.
Ya ce, “Yayin da harkokin kasuwancinmu ke ci gaba da bunƙasa, wajibi ne mu ƙara ƙarfafa alhakin da ke wuyanmu na kula da al'umma da mutanen da ke zaune a yankunan da hanyoyin da muke gudanar da ayyukanmu suka ratsa. Kowace ƙarin mota da ta shiga hanya na zuwa da nauyin tabbatar da cewa ba a yi sakaci da tsaro ba.
“Kare rayukan al'umma dole ne ya kasance babban abin da muke bai wa fifiko a dukkan ayyukan sufuri da muke gudanarwa.”
Ali ya tuna cewa kamfanin ya fuskanci ƙaruwar haɗurran ababen hawa a shekarun 2021 da 2022, lamarin da ya sa aka ƙaddamar da wani cikakken shirin inganta tsaron tuki a farkon shekarar 2023 domin magance matsalar.
Ya ce babban ɓangaren shirin shi ne horas da direbobi da ba su ilimin aiki da ƙwarewar da ake buƙata wajen tuka ababen hawa cikin taka-tsantsan.
Ya bayyana cewa shirin ya fara haifar da sakamako a shekarar 2023, lokacin da adadin haɗurran ya ragu da kashi 30 cikin 100 idan aka kwatanta da shekarar da ta gabata.
Kamfanin ya samu ƙarin raguwar haɗurra da kashi 60 cikin 100 daga baya, wanda Ali ya ce hakan na nuna tasirin ci gaba da zuba jari wajen ƙwarewar direbobi, wayar da kan jama'a game da tsaro da kuma bin ƙa'idojin aiki.
A nata jawabin, Shugabar Sashen Lafiya, Tsaro da Muhalli ta Rukunin Kamfanin Siminti na Dangote Ebere Okonkwo, ta sake jaddada cewa kamfanin ba ya lamuntar duk wani haɗarin ababen hawa a kan tituna.
Ta ce ƙudurin kamfanin na tabbatar da tsaro bai tsaya ga ayyukan da yake gudanarwa kai tsaye ba, har ma ya shafi direbobin da ke ƙarƙashin tsarin jigilar kayayyakin kwastomominsa.
Okonkwo ta bayyana cewa kamfanin na ci gaba da ƙarfafa matakan tsaro ta hanyar horas da direbobi, shirye-shiryen wayar da kan jama'a da kuma sa ido kan yadda suke gudanar da ayyukansu, domin inganta tukin da ya dace da rage haɗurran ababen hawa.
Ta buƙaci direbobin da su riƙa tuna munanan illolin haɗurran hanya, musamman tasirinsu na motsin rai, zamantakewa da tattalin arziki ga iyalansu, masoyansu da al'umma baki ɗaya.
A nasa jawabin, Daraktan Talla na Shiyya, Bankole Goerge, ya ce yanke shawara mai kyau yayin tuƙi na iya ceton rayuka, kare iyalai da kuma taimakawa wajen samar da hanyoyi masu aminci a faɗin Najeriya.
Shi ma wakilin Hukumar Kiyaye Haɗurran Hanya ta Ƙasa (FRSC), Ibrahim Zayyan, ya yaba wa kamfanin Siminti na Dangote bisa jajircewarsa wajen horas da direbobin motocin kwastomominsa da kuma inganta bin ƙa'idojin tukin da ya dace.












