Jamhuriyar Dimokuradiyyar Congo (DRC) ta zargi Rwanda da kashe fararen-hula fiye da 1,500 a gabashin DRC tun farkon Disamba, lokacin da 'yantawayen M23 suka ƙaddamar da sabbin hare-hare.
'Yan kwanaki bayan da gwamnatin DRC da Rwanda suka sanya hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ta shiga tsakani a ranar 4 ga Disamba, M23 ta ƙwace babban birnin Uvira, abin da ya sa dubban mutane suka tsere zuwa kan iyaka suna shiga Burundi.
DRC ta zargi Rwanda da goyon bayan 'yantawayen M23. Amma Rwanda ta musanta zargin.
"Alƙaluman wucin-gadi da aka fitar na fararen-hula da suka mutu sakamakon hare-haren Rwanda da aka kai da bama-bamai da jiragen yaƙi marasa matuƙa tun farkon watan Disamba sun nuna kisan fiye da 1,500," a cewar wata sanarwa da DRC ta fitar a ranar Laraba.
Da take Allah wadai da "aikin zalunci da Rwanda ta aikata", DRC ta kuma zargi Kigali da aika "sabbin bataliyoyin Rwanda guda uku" zuwa gabashin lardin Kudancin Kivu, don ci gaba isa ga "yankin Kalemie mai mahimmanci" a lardin kudu maso gabashin Tanganyika da ake haƙar ma'adinai.
Idan M23 ta yi isa zuwa kudu zuwa Tanganyika, ƙungiyar mai ɗauke da makamai za ta samu gindin zama a arewa maso gabashin yankin da aka fi sani da lardin Katanga, wato cibiyar hakar ma'adinai ta DRC.
Tun bayan sake ɗaukar makamai a shekarar 2021, ƙungiyar M23 ta ƙwace yankunan gabashin DRC mai arzikin ma'adinai, inda ta kori dubban mutane daga gidajensu, ta kuma haifar da rikicin jinƙai mai tsanani.
Bayan ƙaddamar da sabbin hare-hare a ranar 2 ga Disamba, bayan dakatarwar watanni shida, ƙungiyar masu ɗauke da makamai ta kwace Uvira a ranar 10 ga Disamba, tare da ƙwace iko da kan iyakar ƙasar da Burundi, ƙawar DRC.
Bayan da Washington ta zargi Rwanda da karya yarjejeniyar zaman lafiya, wadda shugaban Amurka Donald Trump ya kira a matsayin yarjejeniyar "mu'ujiza", duk da harin M23, ƙungiyar ta ce a ranar 17 ga Disamba za ta janye daga birnin mai dubban mutane.
Amma Washington da DRC sun nuna shakku kan sahihancin sanarwar M23, yayin da majiyoyin yankin suka shaida wa AFP a ranar Alhamis cewa mambobin M23 da jami'an 'yansanda sun tsaya sun zauna a Uvira.
A farkon makon nan, sojojin DRC sun ce sun sake ƙwace wasu matsugunan da ke kewaye da Uvira bayan "arangama ta ɓarke."
Ƙwace garin ya zo ne kusan shekara guda bayan da M23 ta ƙwace manyan biranen gabashin Goma da Bukavu, manyan biranen lardunan Arewa da Kudancin Kivu.
A cewar Majalisar Dinkin Duniya, fiye da mutane 80,000 sun tsere zuwa Burundi bayan sake danna kai na M23, wanda ya kuma raba aƙalla mutane rabin miliyan da muhallansu a Kudancin Kivu kawai.













