| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
3 minti karatu
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rubio na matsa wa UAE lamba domin tsagaita wuta a Sudan
Marco Rubio ya buƙaci Abu Dhabi da ta taimaka domin dakatar da yaƙin da ake yi a Sudan, tare da gargaɗin cewa dole ne a dakatar da bai wa mayaƙan RSF makamai.
Sakataren Harkokin Wajen Amurka Rubio na matsa wa UAE lamba domin tsagaita wuta a Sudan
Yayin da yake magana da 'yan jarida a ranar Laraba, Rubio ya ce Washington na yin 'duk abin da za ta iya' don kawo ƙarshen rikicin. / Reuters
15 Nuwamba 2025

Sakataren Harkokin Wajen Amurka Marco Rubio ya jaddada buƙatar ƙulla yarjejeniyar tsagaita wuta domin ayyukan jinƙai a Sudan.

Ya bayyana haka ne a wata tattaunawa ta waya da Ministan Harkokin Wajen Haɗaɗɗiyar Daular Larabawa Sheikh Abdullah bin Zayed Al Nahyan, 'yan kwanaki bayan da ya yi gargaɗi kan cewa ana buƙatar ɗaukar mataki don katse hanyoyin shigar da makamai ga RSF.

Mai magana da yawun Ma'aikatar Harkokin Wajen Amurka Tommy Pigott ya ce Rubio ya 'jaddada muhimmancin cim ma yarjejeniyar domin ayyukan jinƙai a Sudan a lokacin da suke tattaunawa ta waya.

Sojojin Sudan sau da yawa suna zargin UAE da samar da makamai da kuma bayar da sojojin haya ga RSF, zarge-zargen da ƙwararrun Majalisar Ɗinkin Duniya da wasu 'yan majalisar Amurka suka ga alamar akwai ƙamshin gaskiya a ciki.

Yayin da yake magana da 'yan jarida a ranar Laraba, Rubio ya ce Washington na yin 'duk abin da za ta iya' don kawo ƙarshen rikicin.

'Akwai bukatar a yi wani abu don katse shigowar makamai da tallafin da RSF ke samu yayin da suke ci gaba da ƙarawa gaba,' in ji shi.

An tambaye shi ko UAE na cikin ƙasashen da ke samar da makamai, sai Rubio ya ƙi ambata sunanta a fili amma ya ƙara da cewa: 'Mun san waɗanne ɓangarori ke da hannu... shi ya sa suke daga cikin Quad, tare da wasu kasashen da ke da hannu. Zan iya gaya muku daga matakin kololuwa na gwamnatimmu cewa ana gabatar da hujjoji kuma ana matsa wa ɓangarorin da abin ya shafa. Dole ne a dakatar da wannan.'

Ya kuma ce ba ya ƙaryata yiwuwar ayyana RSF ƙungiyar ta'addanci idan hakan zai taimaka domin kawo ƙarshen rikicin.

MDD ta ƙaddamar da bincike, Turkiyya ta nemi a dakatar da fada

Wannan lamari ya faru ne bayan Hukumar Kare Haƙƙin Ɗan’adam ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Jumma'a ta amince da wani kudiri wanda ya kafa wata tawagar bincike don gano take hakkin bil'adama a al-Fasher, babban birnin Arewacin Darfur, wanda RSF ta kwace.

Majalisar ta umarci masu bincike da su gano waɗanda ake zargi da hannu a ta'asar domin a gurfanar da su a gaban shari'a.

Turkiyya, ta hanyar jawabi da wakilinta na dindindin ya yi a Geneva, Burak Akçapar, ta bukaci a dakatar da yaƙi nan take a al-Fasher da kewaye, a kawo ƙarshen hare-hare kan farar-hula, tare da samar da hanyoyin jinƙai yayin da tashin hankali ke yaɗuwa a Darfur da Kordofan.

Rumbun Labarai
Ministan Tsaron Ƙasa na Isra'ila na so a hana kiran sallah a masallatan ƙasar
Iran ta ce ta kama wani jirgin ruwa ɗauke da lita miliyan 4 ta fetur da aka yi fasa-ƙwauri a Gulf
Waiwaye kan 2025: Shekarar kisan ƙare dangi a Gaza da sauran yaƙe-yaƙe a duniya
Yara na mutuwa saboda tsananin sanyi a Gaza
Netanyahu ya shiga Masallacin Ƙudus a bikin Ranar  Hanukkah ta Yahudawa 'don tsokana'
Ruwan sama mai tsanani ya kashe aƙalla mutum 10 a Gaza a cikin kwana ɗaya: WHO
Hamas za ta ci gaba da adana makamanta don kariya daga hare-haren Isra'ila a gaba - Jami'in ƙungiyar
Matar Shugaban Ƙasar Turkiyya ta karrama 'yanjarida Falasɗinawa
Babu zaman lafiya idan Falasɗinawa ba su samu 'yanci ba, in ji Shugaban Afirka ta Kudu Ramaphosa
Jirgin Amurka ya mayar da 'yan Iran 55 zuwa Tehran
Jirgi maras matuƙi na Isra'ila ya kashe Falasɗinawa duk da an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta
Dakarun Isra'ila sun ƙwace kayayyakin tarihi biyar a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye
Cikin Hotuna: An yi bikin auren gomman Falasɗinawa a Gaza a lokaci guda
Rundunar sojin Isra'ila na fuskantar mafi munin matsalar ƙarancin ma'aikata a tarihinta - Janar Brik
Hamas ta ce an kashe masu leƙen asirin Isra’ila huɗu a arewacin Gaza
Sojojin Isra'ila sun yi kisa cikin ruwan sanyi a Jenin, Falasɗinawa sun ambace shi laifin yaƙi
Masu shiga tsakani a yarjejeniyar Gaza suna tattauna mataki na gaba a Masar
Isra’ila ta yi shelar matakin karɓe iko da wani waje mai tarihi a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan
Turai na shirin horas da ‘yan sandan Falasɗinawa 3,000   bayan yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza
Saudiyya ta ce sai an samar da ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta kafin ta ƙulla alaƙa da Isra'ila