Ƙungiyar Tarayyar Turai tana son ta horas da ‘yan sanda Falasɗinawa 3,000 a Gaza a ƙarƙashin wani shiri mai kama da wanda take aiwatarwa a Gaɓar Yamma Da Kogin Jordan da aka mamaye, kamar yadda wani jami’i ya bayyana ranar Laraba.
Za a "buƙaci samar da zaman lafiya a Gaza da muhimmiyar rundunar ‘yan sanda " idan wannan yarjejeniyar tsagaita wutar ta ɗore, in ji jami’in, wanda aka sakaye sunansa.
Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya ya kaɗa ƙuri’ar amincewa da ƙudurin da Amurka ta tsara na ƙarfafa shirin Trump a Gaza — wanda ya ba da damar ɗorewar yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin Isra’ila da ƙungiyar gwagwarmayar Falasɗinawa Hamas tun ranar 10 ga watan Oktoba.
Shirin zaman lafiyar ya ba da izinin samar da runduna na ƙasa da ƙasa da za ta yi aiki da Isra’ila da Masar da kuma sabon rundunar ‘yan sandan Falasɗinawan da aka horas da wajen kare kan iyakokin da kuma Gaza da aka ɗauke wa sojoji.
Ƙungiyar Tarayyar Turai dai da ƙyar take iya tasiri kan yaƙin da Amurka ta shafe shekaru biyu tana yi a kan Gaza sakamakon rarrabuwar kai a tsakanin ƙasashen da ke goyon bayan Tel Aviv da kuma waɗanda ke goyon bayan Falasɗinawa.
Domin ta matsu da sake samun ƙarfin faɗa aji a yankin, Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ce za ta gabatar da shirin horas da ‘yan sanda Falasɗinawa — waɗanda ba su da alaƙa da Hamas — a wani banagre na ƙoƙarin sake mayar da tsaro mao ɗorewa a yankin.
Gyara a gwamnatin Falasɗinu
Har yanzu kimanin ‘yan sanda 7,000 a Gaza sun asmaun albashinsu ne daga gwamnatin tarayyar Nijeriya wanda ke mulkan Gaɓar Yamma da Kogin Jordan da aka mamaye, kamar yadda jami’in ya bayyana.
Da yawa daga cikinsu sun yi ritaya ko kuma ba sa iya aiki, amma za a iya horas da mutum 3,000, a cewarsa.
Za a yi horaswar ne a wajen Gaza, in ji shi.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ta ɗauki nauyin horas da ‘yan sanda a Gaɓar Yamma da Kogin Jordan tun shekarar 2006, da kasafin kudin da ya kai yuro miliyan 13 (misalin dala miliyan 15).
Ministocin Harkokin Wajen Ƙasashen Tarayyar Turai za su tattauna shawarar horaswar ranar Alhamis a Brussels.
Ƙungiyar za ta kuma karɓi baƙuncin wani taron masu ba da tallafi wa Falasɗinu a ranar, wanda zai tattara wakilai 60, ciki har da na ƙasashen Larabawa — amma ban da Isra’ila.
Taron zai bai wa mahalarta damar "tattauna" iya ci-gaban da aka samu kan sauyi a gwamnatin Falasɗinawa, in ji jami’in.
Ƙungiyar Tarayyar Turai ita ce ta babbar mai tamaka wa gwamnatin Falasɗinawa,kuma ta gindaya sharaɗin cewa duk wani tallafi na gaba kawo gyara wanda take ganin yana da muhimmanci ga gwamnatin falasɗinawa ta taka tata rawar wajen samar da mafita ta ƙasashe biyu ga rikicin Isra’ila da Falasɗinu wanda Turai ta daɗe tana goyon baya.


















