| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Yara na mutuwa saboda tsananin sanyi a Gaza
Bayan lalata yawancin gidaje, Isra'ila na ci gaba da hana matsugunan 'yangudun-hijira, tare da katse hanyoyin motoci da kuma taimakon jinƙai na lokacin hunturu a yankin duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma.
Yara na mutuwa saboda tsananin sanyi a Gaza
Yara a Gaza na mutuwa soboda tsananin sanyi / AP
22 Disamba 2025

Yayin da ruwan sama da iska mai ƙarfi gami da tsananin sanyi suka dabaibaye yankin Gaza ta Falasɗinu, aƙalla Falasdinawa 14 sun mutu sakamakon tsananin yanayin hunturu.

Daga cikin waɗanda suka mutu har da yara aƙalla biyar, da jarirai 'yan makonni biyu da wata ɗaya, waɗanda suka daskare har suka mutu a cikin tantuna na wucin gadi da gidaje da suka lalace saboda hana samar da isassun matsugunai da taimakon jinƙai a yankin da Isra’ila ta yi wa ƙawanya.

Guguwar hunturu ta mamaye tantuna ya kuma yayyaga su - waɗanda ba a tsara su don yanayin sanyi ba - yawanci Falasdinawa da aka kora ne suke samun mafaka tun lokacin da Isra'ila ta lalata fiye da kashi 85 cikin 100 na gidaje a faɗin Gaza.

Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta da aka cim ma a ranar 10 ga watan Oktoba, Isra'ila ta ci gaba da katse hanyoyin wucewar motoci, da wuraren zama na wucin gadi, tare da hana shigar da kayayyakin sake gina yankin da sauran abubuwan da ake buƙata na lokacin hunturu, ciki har barguna da tufafi.

A ɓangare guda kuma sojojin Isra'ila sun kai hari kuɗancin Gaza inda suka kutsa kai cikin sansanin ‘yan gudun hijira a tsakiyar Gaza, a wani sabon yanayi na keta karya yarjejeniyar tsagaita wuta.

Majiyoyin yankin sun shaida wa Anadolu a ranar Litinin cewa jiragen yakin Isra'ila sun kai hare-hare ta sama a yankuna da dama a Rafah, a kudu, duk a lokaci guda da harsasai da bindigogi daga motocin soji a sassan arewacin birnin.

A arewacin Gaza kuwa, motocin soji da bulldozers na Isra'ila sun shiga sansanin 'yan gudun hijira na Jabalia, inda sojoji suka janye daga wurin a matsayin wani bangare na yarjejeniyar tsagaita wuta.

A birnin Gaza, motocin soji da aka ajiye a yankin da Isra'ila ke iko da shi sun buɗe wuta a unguwannin da mutane da zama a yankunan da ke gabashin birnin.

ko da yake ba a samu wani rahoton asarar rayuka ba.

Sojojin Isra'ila sun keta daruruwan doka a Gaza, wanda ya yi sanadiyyar mutuwar Falasdinawa 401.

Sojojin Isra'ila sun kashe Falasdinawa kusan 71,000, galibi mata da yara, tare da raunata wasu sama da 171,000 a hare-haren da suka kai a Gaza tun daga watan Oktoban 2023.