Yarima mai jiran gado na Saudiyya Mohammed bin Salman ya ce masarautarsa na son ta dawo da alaƙa da Isra’ila ta wata yarjejeniya mai suna Abrahams Accords da Shugaban Amurka Donald Trump ke jagoranta, amma da farko tana buƙatar “bayyananniyar hanya” ga samun ƙasar Falasɗinu.
"Muna son mu kasance cikin yarjejeniyar Abraham Accords. Amma muna son mu samu tabbacin cewa mun samu hanyar samar da zaman lafiya ta hanyar kafa ƙasashe biyu," kamar yadda yarima mai jiran gadon na Saudiyya, ya bayana a fadar White House inda ya gana da Trump ranar Talata.
"Za mu yi aiki a kan wannan, domin tabbatar da cewa za mu shirya yanayi mai kyau nan ba da jimawa ba," in ji shi.
Yayin da Trump wanda ya ce baƙonsa "na da fata mai kyau ga Abraham accords,” ya sake matsawa, sai yariman ya ce: "Muna son zaman lafiya ga Isra’ilawa. Muna son zaman lafiya ga Falasɗinawa."
"Muna son su zauna lafiya a yankin, kuma za mu yi iya ƙoƙariunmu domin kai wa ga wannan ranar."
Saudiyya dai tana maimaita cewa samar da ƙasar Falasɗinawa ce manufarta.
Netanyahu kuma ya daɗe da adawa da batun samar da ƙasashe biyu masu cin gashin kansu, duk da amince wa ta je-ka-na-yi-ka da y yarjejeniyar tsagaita wuta a Gaza da Trump tya tsara wacce ke tangal-tangal.
Netanyahu na jagorantar gwamnatin wata gamayyar jam’iyyun da ke da magoya baya masu tsattsauran ra’ayi, waɗanda suka yi watsi da kafa ƙasar Falasɗinu, amma suna son Isra’ila ta karɓe iko da Gaɓar Yamma da Kogin jordan.
Jonathan Panikoff, tsohon mataimakin shugaban ɓangaren bayanan sirri na cibiyar nazari kan Gabas Ta Tsakiya mai suna Middle East, ya ce Trump zai yi kira ga bin Salman ya matsa kusa da daidata dangantaka da Isra’ila, kuma duk wani rashin ci-gaba a wannan fannin ba zai hana ƙulla sabuwar yarjejeniyar tsaro tsakanin Amurka da Saudiyya ba.
"Buƙatar Shugaba Trump ta sanya jari a Amurka, wadda yarima mai jiran gadon ya yi alƙawarin zubawa a baya, za ta iya samar da yanayi na faɗaɗa dangantaka ta tsaro yayin da shugaban zai yi ƙoƙarin dawo da dangataka tsakanin Saudiyya da Isra’ila," in ji Panikoff, wanda yanzu yake cibiyar nazari ta Atlantic Council a Washington.


















