| Hausa
GABAS TA TSAKIYA
2 minti karatu
Netanyahu ya shiga Masallacin Ƙudus a bikin Ranar Hanukkah ta Yahudawa 'don tsokana'
Manyan 'yan siyasa na Falasɗinu sun yi tir da shigar Firaminista Israila masallacin suna mai cewa tsokana ce ta sa ya yi hakan, a daidai lokacin da Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna ke ƙara kutsawa da mamayar Gabashin Birnin Ƙudus.
Netanyahu ya shiga Masallacin Ƙudus a bikin Ranar  Hanukkah ta Yahudawa 'don tsokana'
Netanyahu ya shiga Masallacin Ƙudus a bikin Ranar Hanukkah ta Yahudawa 'don tsokana' / Reuters
9 awanni baya

Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya shiga cikin ginin Masallacin Ƙudus a Gabashin Birnin Ƙudus da aka mamaye a ranar Talata, a lokacin bukukuwan ranar Yahudawa ta Hanukkah, wadda hukumomin Falasɗinu suka yi masa kakkausar suka don suna ganin matakin a matsayin na son tayar da hankali da gangan.

A wata sanarwa, Gwamnatin Birnin Ƙudus ta yi Allah wadai da bayyanar Netanyahu a wurin—musamman a Bangon Yamma, wanda Musulmai ke kira Bangon Al-Buraq—inda ta kwatanta hakan a matsayin “sabon mataki mai tayar da hankali” wanda ke ƙara tsananta tashin hankali a ɗaya daga cikin wuraren ibada mafi tsantseni a yankin.

Ofishin Netanyahu ya wallafa hotuna na firaministan a Bangon Yamma tare da manyan jami'ai, ciki har da Jakadan Amurka Mike Huckabee.

Yahudawa 'yan-kama-wuri-zauna suna ci gaba da tsokana

Bangon wani ɓangare ne na Masallacin Ƙudus, wanda Musulmai ke girmamawa a matsayin wurin ibada na uku mafi tsarki a Musulunci, yayin da Yahudawa ke ganinsa a matsayin waje mai tsarki su ma na addininsu wato (Temple Mount).

A lokacin bukukuwan Ranar Hanukkah na kwanaki takwas, daga 14 zuwa 22 ga Disamba, an shaida ƙaruwar ayyukan masu kafa sansanoni ba bisa doka ba.

Hukumomin Falasɗinu sun ce aƙalla masu kafa haramtattun sansanoni 210 na Isra'ila sun shiga hadadden sansanin Al-Aqsa tun ranar Litinin domin gudanar da taron bukukuwan.

Al-Aqsa ya dade yana zama wani cibiyar tashin hankali tsakanin Isra'ila da Falasɗinu, inda Falasɗinawa ke gargadi cewa ziyarar manyan shugabannin Isra'ila da ƙaruwar masu kafa sansanoni ba bisa doka ba na barazana ga yarjejeniya mai rauni ta kula da tsarin wurin.

Isra'ila ta mamaye Gabashin Birnin Ƙudus a Yakin Larabawa da Isra'ila na 1967 kuma ta ƙwace birnin a 1980, matakin da al'ummomin ƙasa da ƙasa ba su taɓa amincewa da shi ba.

Falasɗinawa na ganin Gabashin Birnin Ƙudus a matsayin babban birnin wata ƙasar Falasɗinawa mai zaman kanta a nan gaba.