Me ke damun Lamine Yamal: Ciwon mara, bakar kaddara, ko taruwar gajiya?
WASANNI
4 minti karatu
Me ke damun Lamine Yamal: Ciwon mara, bakar kaddara, ko taruwar gajiya?Bayan buga wa Barcelona da tawagar ƙasarsa Sifaniya wasanni sama da 130 Lamine Yamal ya fara nuna alamun rauni da gajiyawa, inda ya kasa buga wasanni a 'yan kwanakin nan.
Shekarar Yamal 18 da wata biyu zuwa Okoban 2025 / AP
7 Oktoba 2025

Yayin da ake shirin fara wasannin tawagogin ƙasashen duniya, taurarin ƙwallo za su yi ƙoƙarin taimaka wa ƙasashensu samun cancantar shiga gasar kofin duniya ta baɗi a Amurka, Canada, da Mexico.

Sai dai ‘yan wasa irinsu Lamine Yamal na Sifaniya, za su zura ido ne su gani ana yi, saboda matashin ɗan wasan da ke buga wa Barcelona wasa na fama da jinya tun farkon Oktoban nan.

Rahotanni na cewa ɗan wasan mai shekaru 18 yana fama da ciwo a mara da matsematsinsa, wanda ya tilasta masa ɗaukar hutun makonni daga ƙwallo don samun murmurewa.

Yamal ya samu raunin baya-bayan nan yayin wasan Barca da Paris Saint-Germain na gasar Zakarun Turai wanda suka yi rashin nasara da ci 2-1 ranar 1 ga Oktoba.

Raunin da Yamal ya samu a mararsa abu ne da ba yau ya fara ba, kuma ana ganin zai iya barazana ga lafiya da kuzarin ɗan wasan mai farin jini a nan gaba.

Akwai raɗe-raɗi kan takamaiman abin da ke damun Lamine Yamal, saboda masu cewa rauni ne, ko taruwar gajiya ce, ko kuma dabarar kocin Barcelona ce ta hana shi buga wa Sifaniya wasa.

Akwai ma masu cewa baƙar ƙaddara ce ta fara kama Yamal, sannan akwai masu ganin halayyar ɗan wasan ta ƙashin-kai da neman mata ce ke jawo masa matsalar lafiya.

Taruwar gajiya

Bayan nazarin rayuwar ɗan wasan, wasu masana ƙwallo na ganin gajiya ce ta fara cim masa, sakamakon yadda Yamal ya fara buga ƙwallo a ajin ƙwararru tun bai cika shekara 18 ba.

Ƙididdiga ta nuna cewa lamine Yamal ya buga wasanni 130 a ajin ƙwararru, inda ya kwashe mintuna 8,158 yana taka leda zuwa lokacin da ya cika shekara 18.

Wannan ce babbar hujjar masu ganin cewa ɗan wasan ya tara gajiya tun ƙarfinsa bai gama kawowa ba, kuma hakan abin tsoro ne ganin yadda yake da tagomashi da nasarori a gabansa.

Masana ƙwallo sun ce a tarihi ko kusa, babu wani babban ɗan wasa da ya buga irin wasanni masu yawa haka gabanin cikarsa shekara 18.

Irin wannan zarra da Yamal ya yi, ƙungiyar FIFPRO ta gamayyar ‘yan wasan ƙwallo na duniya ta yi wani nazari kan kuzarin ɗan wasan, inda ta auna adadin mintunan da ya buga wa Barcelona da Sifaniya.

A 2024-25, FIFPRO ta fitar da rahoto mai shafuka 51 mai taken "An Gajiyar Da Shi Kuma Ba a Ba Shi Isasshiyar Kariya ba - Tasiri Kan Lafiya da Kuzarin Ɗan Wasa."

An ambato Dr. Darren Burgess, shugaban wani kwamitin FIFPRO na cewa, wasan ƙwallo "ya ƙara tsananta kan ‘yan wasan da suka daɗe suna aiki, amma ga matasa ‘yan shekara 16 zuwa 20, haɗarin ya fi muni".

Ya yi nuni da yadda yara ‘yan wasa ke cikin matakin da jiki da ƙwaƙwalwarsu ke girma, amma suke fuskantar tsananin buƙatar buga jerin wasanni, da atisaye mai wahala, har ta kai abin ya yi tasiri ga kuzari da daɗewar rayuwarsu ta ƙwallo."

Warkewar Yamal

A halin yanzu da ake fatan ganin Lamine Yamal ya warke ya dawo filin wasa, ana tararrabin ko zai murmure kafin buga babban wasan hamayya na Barcelona da Real Madrid ranar 26 ga Oktoba.

Tuni dai ɗan wasan ya fara lashe kyautukan bajinta a filin wasa, amma fa jikinsa yana gaya masa kan yadda yake take leda cikin yayye da waɗanda ma suka haife shi.

Ana kwatanta Yamal da wasu matasan ‘yan wasa a Turai, kamar Gavi, Pedri da Jude Bellingham. Ga misali, Bellingham bai cika buga adadin wasanni 100 ba sai da ya haura shekara 18 da wata 10.

A tarihi, Yamal ne ɗan wasa mafi yarinta da ya cim ma buga wasanni 100 tun yana shekara 17 da watanni bakwai, inda ya shafe tarihin da Romelu Lukaku ya kafa da watanni huɗu.

A Afrilun 2023 ne Lamine Yamala ya fara taka wa Barcelona wasa yana da shekara 15 da wata tara da kwana 16, a wasan Barcelona da Real Betis.

Kuma tun bayan nan, wasa 18 ne kawai bai buga wa Barcelona da ƙasarsa Sifaniya ba. Sai dai ƙididdigar shafin Transfermarkt ta ce ya kwashe kwanaki 133 baya wasa saboda jinya zuwa yau.