| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za ta warware rikicin Masarauta
Waiya ya jaddada cewa gwamnati na daukar matakai na gaske don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar.
Gwamnatin Jihar Kano ta tabbatar da cewa nan ba da jimawa ba za ta warware rikicin Masarauta
Yaushe za a kawo karshen takaddama kan masarautar Kano? / TRT Afrika Hausa
kwana ɗaya baya

Gwamnatin Jihar Kano ta yi alƙawarin warware rikicin masarautun da ke ci gaba da faruwa wanda ya zama sanadin ce-ce-ku-ce a faɗin ƙasar.

Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida, Ibrahim Waiya ne ya bayar da wannan tabbacin a lokacin da yake ganawa da manema labarai a Kano ranar Alhamis.

Waiya ya jaddada cewa gwamnati na daukar matakai na gaske don dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali a cikin jihar.

Rikicin masarautar ya haifar da damuwa a tsakanin jama'a, “kuma gwamnati na da sha'awar magance wadannan matsalolin cikin gaggawa.”

"Mun kuduri aniyar tabbatar da cewa an warware wannan lamari cikin lumana kuma ba zai kara ta'azzara ba," in ji shi.

Kwamishinan ya nuna muhimmancin tattaunawa wajen warware rikice-rikice, yana mai nuna cewa gwamnati a shirye take ta tattauna da duk masu ruwa da tsaki a harkokin masarautar.

Sasantawa don warware taƙaddama

A jawabinsa, Waiya ya sake nanata jajircewar gwamnati wajen yin mu'amala da cibiyoyin gargajiya da shugabannin al'umma.

Ya lura cewa gwamnati ta fahimci muhimmancin waɗannan ƙungiyoyi wajen kiyaye jituwa da kwanciyar hankali a Kano. "Hanyarmu ta samo asali ne daga girmama bin doka da kuma muradun jama'ar Kano," in ji shi.

Rikicin masarautar ya samo asali ne daga rashin jituwa kan shugabanci ba siyasa da iko, wanda a wasu lokutan ya haifar da rikicin jama'a.

Kalaman Waiya sun zo ne a daidai lokacin da ake buƙatar haɗin-kai tsakanin ƙungiyoyi daban-daban a cikin Jihar Kano da kuma sauya shekar da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi daga Jam’iyyar NNPP zuwa ta APC.

Rikicin masarautar Kano ya fara ne a 2019 lokacin da Gwamnan Jihar na lokacin, Abdullahi Umar Ganduje ya rarraba masarautar tare da sauke Sarki Muhammadu Sanusi na II ya ɗora Sarki Aminu Ado Bayero.

Da Gwamna Abba ya hau mulki a 2023 a ƙarƙashin Jam;iyyar NNPP sai ya sauke Aminu Ado ya mayar da Sarki Sanusi.

Amma tun lokacin ake ta samun dambarwa inda ake zargin tsagin su Ganduje daga APC da goyon bayan Sarki Aminu har ma da ba shi Gidan Sarki na Nasarawa don ya zauna a can yana gudanarf da mulki.