| Hausa
AFIRKA
2 minti karatu
Somaliya ta ce an mayar da tallafin abincin da aka ƙwace ga hukumar WFP bayan takun saƙa da Amurka
A farkon watan nan ne Amurka ta dakatar da duk wani tallafi da take bai wa Somaliya bayan rahotannin da ke cewa jami'an yankin sun kwace tallafin abincin da masu ba da gudummawa suka dauki nauyinsa a wani rumbun ajiyar abinci na WFP da ke Mogadishu.
Somaliya ta ce an mayar da tallafin abincin da aka ƙwace ga hukumar WFP bayan takun saƙa da Amurka
An kiyasta cewa mutane miliyan 4.6 na fuskantar matsanancin karancin abinci a Somaliya. / Reuters
27 Janairu 2026

Gwamnatin Somaliya ta ce an mayar da tallafin abinci da aka ɗauke daga wani rumbun ajiya yayin ayyukan faɗaɗa tashoshin jiragen ruwa a babban birnin Mogadishu ga Hukumar Abinci ta Duniya (WFP), bayan rahotannin da ke cewa jami'an yankin sun kwace tallafin abinci da masu ba da gudummawa suka bayar.

"An mayar da kayayyakin da aka ɗauke daga rumbun ajiya ga Hukumar Abinci ta Duniya gaba ɗaya," in ji ma'aikatar harkokin wajen Somaliya, tana mai ƙari da cewa gwamnati "ta ɗauki alhakin dukkan wannan mummunan al’amari da ya auku kuma ta yi takaicin faruwarsa."

A farkon watan nan ne Amurka ta dakatar da duk wani taimako ga gwamnatin Somaliya, tana mai zargin cewa jami'an Somaliya "sun lalata rumbun ajiya na Shirin Abinci na Duniya (WFP) wanda Amurka ke tallafawa kuma sun kwace tan 76 na tallafin abinci da masu ba da gudummawa suka bai wa 'yan Somaliya marasa galihu."

Jami'an Amurka sun ƙara da cewa duk wani taimako da za a yi nan gaba zai "dogara ne kan Gwamnatin Tarayyar Somaliya ta ɗauki alhaki" sannan ta sa ido kan lamarin.

Babban rumbun ajiya

A ranar Litinin, gwamnatin Somaliya ta ce ta samarwa WFP babban rumbun ajiya wanda zai dace buƙatun ta a yankin tashar jiragen ruwa ta Mogadishu don inganta ƙarfin ajiya da yanayin rarraba kayayyaki.

Hakan zai taimaka wajen tabbatar da ci gaba da isar da tallafin jinƙai da tsaro da kuma rashin katsewar ayyuka," in ji gwamnati.

Da farko ma'aikatar harkokin wajen Somaliya ta ce ayyukan faɗaɗa tashoshin jiragen ruwa da ake yi ba su shafi rumbun ajiyar da ke yankin tashar jiragen ruwa ta Mogadishu ba. inda ta ce, tallafin abincin yana ƙarƙashin kulawar Hukumar Abinci ta Duniya.

A 'yan watannin nan, takun sakar da ke tsakanin Somaliya da Amurka ta sa Washington ta yi wa 'yan Somaliya a Amurka kakkausar suka, inda ta taso su a gaba a ci gaba da fatattakar ‘yan cirani a Minnesota da kuma zarginsu da hannu dumu-dumu da zamba a shirin tallafa wa al'umma a yankin jihar ta tsakiyar yamma inda al’ummar Somaliya su fi yawa a kasar da kusan mutum 80,000.

A watan Nuwamba, Shugaban Amurka Donald Trump ya kawo ƙarshen ba da shaidar zama na ɗan lokaci ga 'yan Somaliya a ƙasar, yana zarginsu da tayar da zaune tsaye, inda ya yi ƙari da cewa "a mayar da su inda suka fito."