| Hausa
NIJERIYA
2 minti karatu
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta ceto mutum 22 daga hannun masu safarar mutane a  Katsina
Kwamandan rundunar a kan iyakar Jibia, Haruna Zakirai, ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai a Daura.
Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya ta ceto mutum 22 daga hannun masu safarar mutane a  Katsina
NIS / Others
26 Janairu 2026

Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya a Daura, ta ceto mutum 22 daga hannun masu safarar mutane a yankin iyakar Zango na jihar Katsina.

Kwamandan rundunar a kan iyakar Jibia, Haruna Zakirai, ya bayyana hakan a lokacin wani taron manema labarai a Daura.

Ya ce an gudanar da aikin ceton ne bayan samun bayanai daga wasu al'ummomin kan iyaka wadanda suka lura da zirga-zirgar da masu safarar ke yi yayin da suke kokarin safarar wadanda abin ya shafa ta kan iyaka.

A cewar Zakirai, jami'an hukumar da na rundunar 'yan sandan Daura sun mayar yi gaggawar kai ɗauki tare da ceto wadanda abin ya shafa a wani gini da ba a kammala ba a kauyen Maibara da ke karamar hukumar Zango ta jihar.

Ya bayyana cewa wadanda abin ya shafa sun haɗa da mata 11 da maza 11, masu shekaru tsakanin 17 zuwa 35, daga sassa daban-daban na kasar, ciki har da jihohin Legas, Osun, Rivers, Kwara, Katsina, Imo, Ondo, Benue, da kuma Babban Birnin Tarayya Abuja.

"Binciken farko ya nuna cewa ana safarar wadanda abin ya shafa ta hanyoyi marasa tsari zuwa Libya sannan sai a wuce da su Turai. An jawo wadanda abin ya shafa da alkawarin samun damar tattalin arziki mai kyau."

Wannan ita ce dabarar da kungiyoyin masu safarar mutane ke amfani da ita wajen jawo hankalin wadanda abin ya shafa ba tare da an sani ba.

Muna kira ga jama'a da su guji wannan tarko. Hukumar Shige da Fice ta Nijeriya a shirye take ta karya wadannan kungiyoyin tare da ceto wadanda aka yi safararsu," in ji shi.

Zakirai ya bayyana cewa wani dan kasar Togo yana cikin wadanda aka ceto kuma za a mayar da shi Togo bayan kammala bincike.

Ya kara da cewa babban jami'in kungiyar masu safarar, wanda aka fi sani da "Cargo," ya tsere kafin kama shi kuma a halin ana nemansa ruwa-a-jallo.

Mai kula da hukumar ya sake jaddada kudirin hukumar NIS na yaki da safarar mutane, shige da fice ba bisa ka'ida ba, da laifukan ketare iyaka, yayin da yake kira ga jama'a da su samar da sahihan bayanai game da wadanda ake zargi da safarar mutane ga hukumomin tsaro.