| Hausa
TURKIYYA
3 minti karatu
Turkiyya ta goyi bayan Nijeriya a yaƙi da ta'addanci yayin da Erdogan ya karbi baƙuncin Tinubu
Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu yana ziyarar aiki ta kwana biyu a Turkiyya26 zuwa 28 ga Janairu.
Turkiyya ta goyi bayan Nijeriya a yaƙi da ta'addanci yayin da Erdogan ya karbi baƙuncin Tinubu
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya tarbi Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu a wani gagarumin bikin tarba na hukuma a Ankara / AA
27 Janairu 2026

Turkiyya ta yi alkawarin goyon bayan Nijeriya a yaki da ta'addanci, inda Shugaba Recep Tayyip Erdogan ya ce Ankara ta duba zaɓuka na ƙara hadin-gwiwa a horon soja da leken asiri yayin tattaunawa da Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu.

"A shirye muke mu yi aiki da Nijeriya a muhimman ɓangarorin da Turkiyya ta goge a kansu na yaki da ta'addanci,' in ji Erdogan, yana mai cewa kungiyoyin 'yan ta'adda, musamman a yankin Sahel na Afirka, suna zama barazana ga kwanciyar hankali a nahiyar.

A yayin jawabi ga manema labarai a taron hadin-gwiwa a ranar Talata bayan tattaunawar a Ankara, Erdogan ya ce an kuma tattauna batun kasuwanci, makamashi, jari, ilimi da masana'antar tsaro, inda ya maimaita ƙudurin kasashen biyu na cim ma mu'amalar ciniki tsakaninsu ta dala biliyan biyar.

'Turkiyya na goyon bayan zuba jari a Nijeriya kuma tana maraba da hadin-gwiwa tsakanin Hukumar Mai ta Turkiyya, BOTAS (kamfanin Turkiyya), da kamfanonin makamashi na Nijeriya,' yana nuni da cewa kasar ta Afirka na da damar zama babbar mai samar da mai da iskar gas a nahiyar.

Shugaban Turkiyya ya kuma jaddada muhimmancin ilimi a dangantakar kasashen biyu.

“Muna farin cikin karbar dimbin daliban Nijeriya a Turkiyya,' in ji Erdogan, yana cewa sabuwar yarjejeniyar da aka rattaba hannu za ta kara karfafa hadin kan ilimi.

Ya kuma yaba da haduwar tawagar Nijeriya da manyan kamfanonin tsaron Turkiyya a lokacin ziyarar.

Kafin sannan, an fara yi wa Tinubu tarba ta musamman a wani biki da aka yi masa faretin sojojin da mahaya dawaki guda 103 a hanyarsa ta zuwa Fadar Shugaban Kasa, wata alama ta tunawa da cika shekarar 103 na Jamhuriyar Turkiyya.

Erdogan ya tarbi Tinubu da kansa a babbar harabar shiga fadarsa, inda shugabannin suka tsaya don rero taken ƙasashensu da kuma kiɗan sojoji.

Shugabannin biyu sun tsaya don daukar hoto a gaban tutocin ƙasashensu kafin su ci gaba da tattaunawa da ta kungiyoyi daban-daban.

Tinubu na kan wata ziyarar aiki a Turkiyya daga 26 zuwa 28 ga Janairu, a lokacin da ake sa ran bangarorin biyu za su sanya hannu kan yarjejeniyoyin hadin gwiwa da kuma tattaunawa da shugabannin kasuwanci da masana'antar tsaro don zurfafa dangantakar dabaru.

Ziyarar Tinubu za ta hada da tarurruka da za su mai da hankali kan sake duba dangantakar Turkiyya da Nijeriya, musayar ra'ayoyi game da batutuwan yankin da na duniya, da sanya hannu kan yarjejeniyoyin da suke nufin kara karfafa hadin gwiwa, in ji Shugaban Harkokin Sadarwa na Turkiyya Burhanettin Duran a wani rubutu a dandalin sada zumunta na Turkiyya NSosyal.

Ya kara da cewa za a gudanar da wani taron zagaye tsakanin Tinubu da shugabannin kasuwanci, da kuma tattaunawa da wakilan masana'antar tsaro a kan iyakar ziyarar.