Rahotanni daga ƙungiyar Chelsea a London na cewa a shirye matashin ɗanwasan gaba, Cole Palmer yake ya koma Manchester United da ke birni Manchester na Ingila.
Ɗanwasan mai shekaru 23 haifaffen garin Manchester ne, kuma ya bayyana rashin jin daɗin ci gaba da zamansa a birnin London, kasancewar yana kewar gida.
Sai dai duk da cewa Palmer tsohon ɗanwasan Manchester City ne, ya ce baya mararin komawa can. Amma dai a shirye yake ya sauya sheƙa zuwa Manchester United.
Manchester United dai ita ce ƙungiyar da Plamer yake goyon baya sanda yana ƙarami.
A wani ɓangaren kuma, Liverpool ta ce ba ta da niyyar raba gari da kyaftin ɗinta, gwarzon ɗanwasan baya, Virgil van Dijk mai shekaru 34.
Liverpool ta ce ba za ta saurari duk wani tayin ɗauke Van Dijk ba a kakar bana, kasnacewar kyaftin ɗin yana da kwantiragi har zuwa bazarar 2027.
Sai dai Liverpool ɗin a shirye take ta raba gari da wani ɗanwasan bayan daban, Andy Robertson wanda ke samun tayi daga Tottenham.
A baya dai an tsara Robertson mai shekaru 31 ya zauna, amma yanzu Liverpool na shirin dawo da ɗanwasan baya, Kostas Tsimikas daga aro a Roma.
Hakan na nufin idan wannan shirin ya tabbata, Robertson zai iya tafiya Tottenham.










