A ranar Talata Turkiyya da Najeriya sun amince su zurfafa haɗin gwiwa a fannoni daban-daban na masana'antu, kasuwanci, zuba jari da tsaro, inda suka bayyana sabbin hanyoyin da za su ƙara kyautata dangantakar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
Ministan Ciniki na Turkiyya Omer Bolat ya ce Ankara da Abuja sun sanya hannu kan yarjejeniyar haɗin gwiwa ta kafa Kwamitin Tattalin Arziki da Ciniki na Haɗin gwiwa (JETCO), tare da yarjejeniyar fahimtar juna kan kayayyakin more rayuwa na Halal, bayan tattaunawar da aka yi a lokacin ziyarar aiki ta shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya kai Turkiyya.
"Mun tattauna batutuwa da dama waɗanda za su ƙara zurfafa haɗin gwiwarmu a fannonin masana'antu, kasuwanci, zuba jari da kuma samar da kayayyaki," in ji Bolat a cikin wata sanarwa, inda ya ƙara da cewa yarjejeniyar za ta samar da sabbin damarmaki ga 'yan kasuwa a ƙasashen biyu.
An sanya hannu kan yarjeniyoyi 9
Bolat ya ce ɓangarorin biyu suna aiki don cim ma burin cinikayya ta dala biliyan 5, inda suka yi alƙawarin faɗaɗa harkokin kasuwanci, haɓaka zuba jari da kuma ƙarfafa haɗin gwiwa tsakanin kamfanoni masu zaman kansu.
Turkiyya za ta ci gaba da hulɗa da Najeriya "bisa ga aminci da kuma tsarin haɗin gwiwa na dogon lokaci," in ji shi.
An sanya hannu kan yarjejeniyoyi tara jimilla a gaban Shugaba Recep Tayyip Erdogan da Tinubu bayan tarurrukan haɗin gwiwa a Ankara.

Yarjejeniyar ta ƙunshi horar da sojoji, samar da tsaro, manufofin ƙasashen waje, kafofin watsa labarai da sadarwa, manyan makarantu, shaidar amincewa da ingancin abincin halal, horar da jami’an diflomasiyya, da harkokin zamantakewa da inganta rayuwar mata.
Tinubu ya ce Nijeriya na da niyyar zurfafa haɗin gwiwa da Turkiyya, musamman a fannin tsaro da cinikayya, yana mai ambaton ƙoƙarin da aka yi na yaƙi da rashin zaman lafiya da haɓaka ci-gaban tattalin arziki.
Ƙarfafa dangantaka
Cinikayya tsakanin kasashen biyu ta kai dala miliyan 688.4 a cikin watanni 11 na farko na shekarar 2025.
Manyan ɓangarorin da aka fi cinikayya tsakanin ƙasashen biyu a shekarar da ta gabata sun haɗa da makamashi inda Najeriya ta zama babbar abokiyar cinikayya ta Turkiyya a yankin kudu da hamadar Sahara.
Haɗin gwiwar tsaro ya karu cikin sauri, inda Rundunar Sojan Sama ta Najeriya ta sayi jiragen sama marasa matuki kirar Turkiyya da kuma jiragen helikwafta guda shida samfurin ATAK T129.
Kamfanonin Turkiyya suna aiki a fannonin gine-gine, makamashi, tufafi da masana'antu a Najeriya, yayin da kamfanoni sama da 50 mallakar Turkiyya suka zuba jarin kimanin dala miliyan 400 a ƙasar.
Darajar ayyukan da 'yan kwangilar Turkiyya suka yi a Najeriya ya kusa kai dala biliyan 3.
Turkiyya da Najeriya sun kafa dangantakar diflomasiyya a shekarar 1960 kuma sun ci gaba da fadada hadin gwiwa, musamman a fannin tsaro, yayin da Abuja ke kara karfafa yakin da take yi da kungiyoyin 'yan ta'adda.















